Tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa kuma Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Yamma Alhaji a karkashin Jam’iyyar APC, Abdullahi Adamu ya ce ba don Buhari yana zabi a yakin da yake yi da cin hanci da rashawa ba da tuni ya daure tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Sanata Abdullahi Adamu yana mayar da martani ne kan wasikar da Cif Obasanjo ya rubuta yana neman Shugaba Buhari kada ya sake tsayawa takarar Shugaban kasa a zaben badi, inda ya ce tsohon Shugaban kasar bai da muru’ar da zai bayar da irin waccan shawarar.
“Cif Obasanjo ya ce Shugaba Buhari yana zabe a yakinsa da cin hanci da rashawa. Na yarda da shi, domin in da Shugaban kasar ba ya zabe, da shi kansa Cif Obasanjo yanzu yana tsare yana fuskantar shari’a kan cin hanci da rashawa, musamman cin hancin da ya bayar a Majalisar Dokokin ta kasa a shekarar 2006 a kokarinsa na neman tazarce karo na uku,” inji Sanata Adamu.
Sanata Adamu ya kara da cewa: “Shi kansa (Obasanjo) ya sani kamar yadda ni da sauran manyan ’ya’yan Jam’iyyar PDP muka sani, ido a rufe ya nemi hakan har ya bullo da gyaran tsarin mulki. Ya ba kowane dan Majalisar Dokoki ta kasa Naira miliyan 50 don su goyi bayan gyaran tsarin mulkin. Sababbin kudi kar aka kai a cikin akwatunansu daga taskar Babban Bankin Najeriya aka rarraba wa ’yan majalisar. Kudin ba nasa ba ne, kuma Majalisar Dokoki ta kasa ba ta san da kasafinsa ba kamar yadda doka ta nema, na amince gaza sanya tsohon Shugaban kasar ya yi bayani kan kudin, Shugaba Buhari yana nuna zabi a yakinsa kan cin hanci da rashawa.”
Ya ce, “Kuma kada mu manta Shugaba Buhari ya ki damuwa ya tuhumi Obasanjo kan rawar da ya taka a kan badakalar Halliburton wadda Amurkawa suke tsare a kanta. Kuma akwai bukatar Buhari ya waiwayi batun kamfanin Siemens wanda aka samu gwamnatin Obasanjo da laifi a kansa.”
Sanata Adamu ya ce Obasanjo yana yawan sukar wadanda suka biyo bayansa a mulki tun lokacin da ya bar mulki a matsayin Shugaban kasa na soji.
“Tun Oktoban 1979 da ya bar mulkin da ya samu yabo a gida da waje, sai Obasanjo ya rika sukar duk wata gwamnati ta bayansa. Ya nada kansa wani waliyi a kasar nan. Yana ganin yana da hikima irin ta Annabi Sulaiman don haka ya ba kansa matsayin wanda ya fi cancantar ya yanke shawara kan wane ne zai mulki kasar nan,” inji Sanatan.
“Kuma a wani bangare na wannan dalili ne kafin ya sauka daga mulki a shekarar 2007, jam’iyyarsa ta PDP ta ba shi mukamin ‘Wanda ya yi sabuwar Najeriya kuma Uban kasa.” Wannan mukami ya sa sa mutum ya rika jiji-da-kai ya rika ganin shi wani waliyyi ne,” inji shi.