✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kamaru za mu koma muddin Peter Obi ya fadi zaben 2023 – Babachir

Babachir, ya ce bai san me APC take ba da ta gaza korarsa daga jam'iyyar.

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya ce shi da wasu jiga-jigan siyasa kasar Kamaru za su koma muddin dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, bai lashe zaben 2023 ba.

Babachir ya bayyana haka ne a yayin wata tattauna wa da Peter Obi da masu ruwa da tsaki na LP daga Arewa maso Gabashin Najeriya a Abuja.

Tsohon Sakataren Gwamnatin ya kuma bayyana mamakinsa da cewa APC ba ta kore shi daga jam’iyyar ba, duk da adawarsa da dan takararta na Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Ya kara da cewa zaben Shugaban Kasa na 2023 ya zama dole Obi ya lashe shi, idan aka yi la’akari da halin da kasar ke ciki.

Babachir ya ce, “Ina cikin APC kuma ina cikin Kwamitin Amintattu na jam’iyyar, amma ina goyon tafiyar Peter Obi da Yusuf Datti. Har yanzu APC ba ta kore ni ba.

“Ban san abin da suke jira ba.

“Muna son Obi ya ci zabe kuma dole ne ya ci wannan zaben. Idan muka fadi wannan zabe, dukkanmu za mu yi hijira zuwa Kamaru saboda kunya da wulakanci na rashin cin nasara.”

Babachir dai ya shiga yin adawa da takarar Tinubu, tun bayan da dan takarar APC ya sanar da daukar Kashim Shettima a matsayin wanda zai yi masa abokin takara.

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyar da wasu sun nuna rashin amincewarsu da takarar Musulmi da Musulmi a matsayin wadanda za su mulki kasar nan, idan har suka ci zabe a 2023.