✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kainuwa

BASHIR YAHUZA MALUMFASHI (08065576011) ya gabatar da wannan waka a ranar Alhamis 24-06-1438BH = 23-03-2017, a yayin gudanar da wani taro da aka shirya wa…

BASHIR YAHUZA MALUMFASHI (08065576011) ya gabatar da wannan waka a ranar Alhamis 24-06-1438BH = 23-03-2017, a yayin gudanar da wani taro da aka shirya wa ’yan jaridar Shoshal-Midiya domin tantance ayyukan da Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya gudanar a cikin shekara biyu da hawansa mulki:

Gwamnanmu Masari,

Aikinka nazari,

Ba ka garari,

Nasara ka zam damkewa.

*

Dankama har Damari,

Ba ka kurari,

Ba ka nasari,

Aikinka kake makawa.

*

Rika riko mai tsauri,

Ka doke tsirari,

Ba su yin tasiri,

Kai ne mai Katsinawa.

*

Masu adawa kuri,

Sun yo tsiriri

Su ne ’yan miriri,

Kai ne mai Daurawa.

*

Dallatu uban taurari,

Ka fi gaban jariri,

A daji akwai mariri,

Aminu mai Katsinawa.

*

Matawallen Hausa kirari,

Ka fi gaban kanari,

Ba ka aikin kari,

Amanar mai Daurawa.

*

Amanar Baba Buhari

Zuciya fara sukari

Ba ka alfahari,

Allah kake rokawa.

*

Farin ruwa mai tsari,

Kana kashe kissa tari,

Ga magabta sanya mari,

Adalci kake aikawa.

*

kyale wancan mai sauri,

Maciji bar shi da sari,

Sullutu o’e Bagwari,

Ka wuce wulakantawa.

*

Zaman lafiya ne jari,

Katsi gidanmu a fari,

Daura gandun alheri,

Sawaba muke nemawa.

*

Mulkinka Aminu Masari

Ka aika ba wadari

Allah ne wutiri.

Jagora Yake badawa!