Daya daga cikin dattawan arewa, Alhaji Bashir Tofa, ya yi Allah wadai kan yadda ake kai wa Fulani hari a jihohin Kudu maso Yammacin kasar nan.
Tofa, ya sanar da haka ne cikin wani jawabi da sanya wa hannu, inda ya ce kisan da ake yi wa Fulani abin kyama ne matuka.
- A karo na biyu Igboho ya jagoranci kone gidajen Fulani
- Rikicin Fulani: Sule Lamido ya kare Buhari
- Saraki ya gargadi Buhari kan rikicin Fulani da Yarbawa
- Kisan Fulani: Babu ruwanmu a sintirin Amotekun —Miyetti Allah
A cewarsa, “Muna Allah wadai da yadda kullum ake kashewa tare da nakasa ’yan arewa, ciki har da Fulani a wasu sassan kasar nan.
“Bayyane yake a fili akwai wasu masu fakewa da wata muguwar akida dake son tada rikici a kasar nan.
“Tashin hankali ya fara kunno kai, idan aka fara ramuwar gayya kan ’yan kudu mazauna Arewa, to da wuya a shawo kan lamarin.
“Makiyanmu dake ciki da wajen kasar nan jami’an tsaro sun san su, so suke mu ci gaba da kashe junanmu.
“Babu wani yanki na wannan kasar dake cikin zaman lafiya, saboda ’yan ta’adda daga ciki da wajen kasar nan na son kassara mana kasa,” cewar Tofa.
Dattijon wanda ya taba tsayawa takarar Shugaban Kasa a shekarar 1993 ya kuma yi kira ga shugaba Buhari da ya dauki matakan gaggauwa don kawo karshen matsalar tsaro da ta kabilanci da suka addabi Najeriya.
Ya ce, “Na tabbata yanzu haka a Fadar Shugaban Kasa ana tattaunawa kan lamarin, amma yana da kyau a gaggauta daukan matakin da ya dace.
“Idan har dan Najeriya ba zai iya zuwa wani yanki ya yi rayuwa ko kasuwanci ba tare da tsangwama ko kashe shi ba, to babu wanda ya kamata ya zauna a wani wajen.
“Wannan shi ne abin da makiyanmu ke so, kuma in har haka ta kasance, to zamu kasance ba mu da kasa, ya kamata mu hana hakarsu cimma ruwa.
“Ya kamata wadancan wawayen su da shugabanninsu dake amfani da su wajen korar wasu daga jihohinsu, su san cewa su ma akwai ’yan uwansu dake zaune a wasu sassan kasar nan.
“Dole ne su daina abin da suke kuma doka ta dauki matakin da ya dace a kansu,” inji Bashir Tofa.
Kira nasa na zuwa ne bayan hare-haren da aka kai wa Fulani a yankin Kudu maso Yammacin kasar nan har sau biyu a cikin mako daya.