Kimanin mutum 1,192 ’yan bindiga suka kashe tare da sace wasu 3,348 a bara a Jihar Kaduna da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Gwamnatin Jihar Kaduna da ta sanar da hakan ta ce cikin wadanda aka kashe akwai maza 1,038 da mata 104 da kuma kananan yara 50.
- Ranar Hijabi: Fitattun mata da aka yi wa tambari a duniya
- ’Yan wasan Kamaru sun bayar da albashinsu ga wadanda turmitsitsin Olembe ya shafa
Wannan dai na kunshe ne cikin rahoto na bayanan tsaro na shekarar 2021 da Gwamna Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya karba daga Maaikatar Tsaron Kaduna a yau Talata.
Kwamashinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida Samuel Aruwan ne ya gabatar da rahoton a fadar gwamnati a wani kwarya-kwaryan taro da ya samu halartar wasu kwamandojin rundunar sojan Najeriya da ke jihar.
Aruwan ya ce yankin Kaduna ta Tsakiya ya yi asarar rayukan mutane 720 a sakamakon hare-haren yan daban daji, rikicin kabilanci da sauran tashe-tashen hankali.
A Kudancin Kaduna kuma kamar yadda Kwamishinan ya bayyana, an tafka asarar rayukan mutane 406 a sakamakon rikice-rikice na kabilanci kari a kan ta’addancin yan daban daji.
A nasa jawabin, Gwamna El-Rufai ya ce bisa la’akari da rahoton tsaron jihar da aka gabatar masa, akalla mutum tara a kullum sun fada tarkon masu garkuwa da mutane a shekarar 2021 da muka yi bankwana da ita.