Masu karatu kamar yadda na yi alkawari a makalata ta makon jiya cewa cikin yaddar Allah zan kawo muku bayanan da suka gabata a ranar Litinin din makon jiya wato 19 ga watan Nuwamba, wajen kaddamar da gangamin neman kuri’a na dan takarar shugabancin kasa a inuwar babbar jam’iyyar adawa ta PDP, da aka yi a waccan rana a Abuja babban birnin tarayya, wato Alhaji Atiku Abubakar tsohon Mataimakin Shugaban Kasa a Jam’iyyar PDP a tsakanin 1999 zuwa 2007. Kundin manufofinsa yana da taken “Shirye-shiryena a kan kasar nan.” Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da nasa a ranar Lahadi 18, ga Nuwamba, mai taken “Mataki na gaba.” Samuwar haka ga manyan ’yan takarar jam’iyyun biyu, bai rasa nasaba da busa usur din da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), don ba da damar gangamin neman kuri’a ga dukan ’yan takarar neman shugabancin kasa da na Majalisar Dokoki ta Kasa daga ranar 18 ga watan na Nuwamba.
A wajen kaddamar da nasa kundi da gangamin neman kuri’ar a Abuja, Alhaji Atiku ya fadi cewa kasar nan tana bukatar jajirtacce, mai da’a da tsananin kishinta, wanda dole ne ya kasance mai tsayuwar daka da zai iya fitar da ita daga cikin mawuyacin halin da take ciki, kasancewar akwai gagarumin aiki, ba wai kwaskwarima ba. Ya kuma sha alwashin kara samar da kudaden shiga ga lalitar gwamnatoci, yana mai ba da tabbacin cewa ba wata jiha da za ta rika samun kudaden shigar da suke kasa da wadanda take samu a yanzu, ta yadda kokarin jiha wajen aiki tukuru shi ne yadda za ta samu kudaden shigarta.
A kan masu zuba jari, dan takarar Shugaban Kasar na PDP, ya sha alwashin kara nemo masu zuba jari, har ma yana cewa “Muddin aka zabe ni, na zama Shugaban Kasa a badi, zan tashi tsaye wajen kara kawo masu zuba jari da tallafa wa masu kanana da matsakaitan sana’o’i miliyan 50 da muke da su yadda za su iya habaka tattalin arzikin kasar nan zuwa Dalar Amurka biliyan 900 daga yanzu zuwa shekarar 2025. Wadannan hanyoyin zuba jari za su samar da ayyukan yi akalla miliyan 2 da rabi duk shekara, baya ga rage radadin talaucin da mutum miliyan 50 suke fama da shi a cikin shekaru biyu,” inji dan takarar na PDP, Alhaji Atiku Abubakar.
Wani alkawari da Alhaji Atiku ya yi wa ’yan kasa a cikin Kundin Neman kuriar nasa mai shafuka 186, har da yadda zai yi amfani da tsarin horar da matasa maza da mata har miliyan 1, duk shekara, tare da rika ba su bashi mai saukin biya kuma cikin dogon lokaci. Ya ma tabo batun cewa irin matakan da zai dauka don kai kasar nan ga tudun mun tsirar da take bukata, masu tsananin tsauri ne da kuma daukar lokaci kafin a kai ga nasarar da suke bukatar juriya.
Yayin da shugaba Buhari ya bayyana irin nasarorin da ya samu a kan alkawuran da ya yi wa ’yan kasa da suka zabe shi a 2015, irin su yaki da cin hanci da rashawa da farfado da tattalin arziki da tsaro da suka tabarbare a wancan lokaci, da inda zai dora idan har an sake zabensa a zaben na badi, shi kuwa Alhaji Atiku Abubakar alkawuran da ya yi na irin ayyaukan da zai yi kamar yadda na kawo wasu daga cikinsu a farko, wanda da ma haka ya kamata, gangamin neman kuri’ar ya kasance tsakanin ’yan takara, wato su tallata hajarsu ga masu bukata.
Amma kuma wani hanzari ba gudu ba, duk da yake na rubuta wannan makala ce daga irin bayanan da na iya karantawa ko na ji ta kafofin watsa labarai, domin har zuwa wannan lokaci da nake rubuta wannan makala ban kai ga ganin kundin manyan ’yan takarar Shugaban Kasar biyu ba. Amma dai na ji jama’a suna ta tsegumin cewa Alhaji Atiku bai ce komai ba a kan yadda gwamnatinsa za ta tunkari babban batun nan na cin hanci da rashawa da ya dade yana kawo tarnaki ga bunkasar tattalin arzikin kasar nan. Cin hanci da rashawa da gwamnatin shugaba Buhari tun farko ta sa shi cikin abubuwa uku da za ta yaka, wanda kuma zuwa yanzu ta fara haska wa ’yan kasa irin yadda wadansu da suka samu madafun iko, musamman a wannan jamhuriyyar suka rika kwasar kudaden gwamnati tamkar kudaden gado.
Idan har akwai wannan niyya ta yaki da cin hanci da rashawa a Kundin Atiku, kuma marubuta jawabinsa, ba su sa da shi ba, to, kuwa ba su cikata aikinsu ba. Domin kuwa yanzu ’yan kasa musamman talakawa sun gamsu da yadda gwamnatin Buhari take yaki da cin hancin da rashawa wanda a karon farko ya haifar da daure tsofaffin gwamnonin jihohin Filato da Taraba Mista Joshua Dariye da Rabaran Jolly Nyame, bayan kotu ta same su da laifuffukan da aka caje su kuma aka same su da aikatawa. Duk da sun daukaka kara zuwa Kotun Daukaka Kara ta Tarayya, suna neman a soke hukuncin kotun baya a kuma sallame su, amma dai dan sassaucin wa’adin daurin da aka yi musu kadai suka samu.
Mai karatu ka iya cewa kamar yadda Shugaba Buhari ya yi sa’a har yanzu mafi yawan talakawan kasar nan suna kaunarsa suna kuma tare da shi a zaben badi, shi ma Alhaji Atiku yana tare da dukan jiga-jigan jam’iyyarsu ta PDP, wadanda karkata su a kansa a zaben fitar da dan takarar neman shugabancin kasa na jam`iyyar da aka yi a Fatakwal a cikin watan jiya, Atikun ya samu nasara a kan sauran abokan takararsa 12. Haka kuma kwatsam a cikin watan na Oktoba sai ga Atiku tare da tsohon maigidansa da ya yi wa mataimaki na shekara 8, tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo, wanda tun kafin su bar gwamnati a shekarar 2007, suka raba gari ya zama ba sa ga maciji, wai sun shirya, har ma da shaidawar wadansu malaman addinai biyu, wato Sheikh Dokta Ahmad Gumi da Rabaran Fada Hassan Kukah.
Wannan shi ne ya tabbatar da karin maganar nan da ake cewa “Siyasa ba ta da aboki ko makiyi na dindindin, sai dai ra’ayi ko bukata ta dindindin. In ban da haka me ya canja, har Cif Obasanjo da ya ce idan har ya goyi bayan Atiku a takarar Shugaban Kasa, to, Allah ba zai taba yafe masa ba, amma ba a kai ko’ina ba, ba kunya, ba tsoron Allah Cif Obasanjo ya canja ra’ayinsa. Da Musulmi yake sai a ce ya yi kaffara, amma kasancewar Obasanjo mai digirin digirgir a kan addinin Kirista na san ya san yadda zai ce da Allah.
Kamar yadda na fadi a makalar makon jiya, zaben na badi zai kasance ne tsakanin ’yan takarar manyan jam’iyyun siyasar kasar nan biyu, wato Muhammadu Buhari na APC da Alhaji Atiku Abubakar na PDP, wadanda dukansu ’yan Arewa ne kuma Fulani kuma Musulmi. Kazalika kowannensu ya daura damara. Samun haka ba ko shakka ya rage tunanin mai tunani na dukan sassan kasar nan a kan wa zai zaba.
Babban abin yi shi ne mu yi ta addu’ar Allah Ya ba mu ikon zaben shagabanni nagari tun daga sama har kasa, amin summa amin.