✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kada ’yan kwallon Eaglets su yi gaggawar fita waje – John Obuh

Tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Golden Eaglets da kuma ta ’yan kasa da shekara 20 (U-20) John Obuh ya ba ’yan kwallon Golden Eaglets…

Tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Golden Eaglets da kuma ta ’yan kasa da shekara 20 (U-20) John Obuh ya ba ’yan kwallon Golden Eaglets da suka lashe gasar cin kofin matasa na duniya da aka kammala a ranar Lahadi da ta wuce shawarar kada su ce za su yi gaggawar tafiya kasashen waje don cigaba da kwallo duk da nasarar da suka samu na lashe kofin.
A wata tattaunawa da kafar sadarwa ta Naij.com ta yi da shi a wayar tarho kocin ya ce duk da yake ’yan kwallon sun yi namijin kokarin wajen lashe gasar cin kofin duniya a karo na biyar ga Najeriya, kada hakan ya rude su su ce sun kware za su bar kasar nan don cigaba da kwallo a kasashen ketare musamman a yankin Turai.  Ya ce kamata ya yi su cigaga da taka leda a gida har zuwa nan gaba a lokacin da za su kware kafin su fice daga kasar nan.  Ya ce abin da ya fi dacewa su yi yanzu shi ne su zauna a gida don su bunkasa gasar rukuni-rukuni na kasa.
Daga nan sai ya shawarci Hukumar kwallon kafa ta kasa watau NFF ta matsa da ’yan kwallon zuwa kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 20 (U-20) don su cigaba da yin kwallo a can.  Ya ce hakan kadai zai bunkasa kwallon kafa a Najeriya.  “A mayar da su kungiyar U-20 don su goge a can kafin su fita kasashen ketare”, inji Obuh.
Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Enugu Rangers John Obuh ya kuma yaba wa kocin Eaglets Emmanuel Amunike, inda ya ce babu shakka kocin ya ba marada kunya.  “Ba a taba tsammanin kocin zai iya kaiwa wasan karshe ba, sai ga shi ya ba kowa mamaki bayan ya lashe kofin”.
kungiyar Golden Eaglets dai ita ce ta biyu wajen lashe kofin sau biyu a jere a tarihin gasar cin kofin duniya na ’yan kasa da shekara 17.
Idan za a tuna kungiyar ce ta lashe kofin da ya gudana a shekarar 2013 a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sai ga shi ta sake dauka a wannan shekara ta 2015.  Kawo yanzu kungiyar ce take kan gaba wajen lashe kofin har sau biyar.