A makon da ya gabata ne Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi na Biyu ya faxi cewa shirye-shiye sunyi nisa wajen gabatar da dokar iyali ga majalisar dokokin Jihar Kano, wadda idan an tabbatar da ita za ta tava batutuwa da suka shafi cin zarafin mata da auren wuri da qarin aure ga marassa hali, a inda har mai martaba ya qarqare da cewa ya samu tabbacin cewa tallauci ne ke haifar da ta’addaci.
A nan ana nufin xaukan batutuwan da ake sa ran dokar ta qunsa na xanyi tsokaci. Dalilin yanayin aiki na da kuma sha’awa ta son kawo ci gaba ga al’umma, ya sa na daxe ina bibiyar harkokin zamantakewar iyali. A bisa qoqarin yin adalci ga maudu’in zan kasa iyalai kashi biyu wato na maraya da na karkara. Sanin kowa ne cewa ana matuqar cin zarafin mata, sai dai dalilan cin zarafin ya babban ta da dama, amma za mu xauki wanda yafi yawaita. Wanda a biranen mu mafi akasari masu cin zarafin matan masu hali ne ko dai manyan ‘yan kasuwa ko kuma manyan ma’aikata kai haitta malamai ma ba a bar su a baya ba, wasu daga cikin waxancan rukunan kan ci zarafin mata ne don sun san suna da halin qara aure sakamakon kwadayi na iyayen ‘ya’ya mata na abin duniya. Wasu kuma kanyi haka ne sanin cewa sun san za su je karkara su auro masu sauqin kuxi ko buqatu.
Su kuwa mutan karkara batun qarin aure a wajen ya zama al’adace tare da nuna isa, kusan duk bayan an yi girbi, amfanin gona yai kyau sai kaji ba abin da ake sai batun qarin aure.
A binciken da na yi na tabbatar da cewa har yanzu a karkarar mu ana auren sadaka da kuma wata al’ada ta sa ranar xaurin aure ba sai da miji ba.
Nau’in cin zarafin shi ma ya danganta da wuri wato maraya ce ko karkara.
A maraya yawanci idan ba ‘yanci rani ba, ba kasafai za ka ji mata na kukan abinci ba, sai dai a kan samu masu hana iyalansu lafiyayen abinci. Tabbas akwai cin zarafi na duka da zagi, wani lokacin ma da hana zuwa asibiti ko yin sana’a ko da ta cikin gida ce. Ga saki barkatai, don na san mutumin da ya auri mata sun fi 20. Akwai wanda ya kori matansa huxu lokaci xaya. Akwai lokaci da muka raba faxa tsakanin ma’aurata mijin na neman yanka matarsa ya shake wuyanta…
A karkara kuwa dama akwai dogaro da kulle, ga hana zuwa asibiti, ga ba abinci mai lafiya, amma fa ba a rashin abinci. Su ma dai akwai dukan mata da zagi.
Amma duk wanxancan matsalolin ba su da alaqa da talauci, don ko a maraya ko karkara duk wanda ka ga yana qara aure to sai ya ga yana da ‘yan mutsabbai tukunna, kamar yadda na faxa a baya. Game da wulaqanta mata kuwa akwai jahilci da kuma rashin sanin kai.
Bincike na ya tabbatar mana da cewa cin zarafin mata na xaya daga cikin masu haifar da mace-macen mata da yara (Maternal and Infant Mortality). A nan hukuma na da laifi don ina mai tabbatar da cewa mafi yawan garuruwan dakatai ba su da asibiti sai xakin shan magani wato sha ka tafi (Dispensary) ballantana asibitin kwanciya ko da mai gado biyar ne, waxanda mafi yawansu ma ba sa aiki yadda ya kamata.
ii. Auren wuri kuwa na da alaqa da jahilci, al’ada da kuma gurguwar fahimta ga addini, a inda za ka ji iyaye na cewa haramun ne ‘ya mace ta fara jini a gidan iyayenta, tare da gudun abin kunya na bin maza. Don haka har yanzu suna buqatar ilimantarwa.
iii. Qarin aure fiye da mace xaya.
Gaskiya ina ra’ayin cewa qarin aure da yawan haihuwa ba shi da alaqa da ta’addaci, don bisa fahimta sakomakon cuxanya da al’umma na fahimci cewa jahilci na taka muhimmiyar rawa wajen lalacewar matasa, don da yawa daga cikin masu ta’addaci za ka same su, kasancewar ‘yan cirani ne, wato sun baro karkara sun dawo maraya don samun abin duniya, wanda shi kansa yawon ciranin yana taka muhimmiyar rawa wajen samar da ‘yan ta’adda (Rural- Urban Migration) da akasarin su za ka ga suna rayuwa a birni ba mai tsawatar musu, don kazo-kazo nazo ne, saboda haka kowannensu na tafi da rayuwarsa ne yadda ya ga dama, don haka shaye-shaye, qwace da ma dukkan nau’ukan ta’adacci suka yawaita.
Ina mai ganin yiwuwar kafa dokar iyali a Jihar Kano bai taso ba, duba da da abubuwan ka iya afkuwa sanadiyyar dokar, misali:
i. Yawaitar mata marasa aure manya da qanana.
ii. Yiwawar yaxuwar laifuffukan zinance-zinace da maxigo da fyaxe da sace-sace da makamantansu.
Iii. Barace-barace da damfara da sauransu.
Idan muka duba sannan muka yi nazarin yadda qasashen da muke qoqarin koyi da su, wato Dubai da Oman da Qatar da Kuwait da Malaysia da Morocco da Saudiyya da kuma UAE dukkanninsu sai da suka tabbatar sun yi maganin matsalar barace-barace da rashin aikin yi. Sai da suka tabbatar da kyautatuwar lafiya da fidda zakka yadda ya kamata. Sannan suka tabbatar da waccan doka, hakazalika dukkaninsu qasashen Labarawa ne masu cin gashin kansu ba jihohi ne ba wanda ke karbar umarni daga tarayya. Ba za mu manta da batun shari’a ba da aka qaddamar, sam barka an samu ci gaba, amma dai ba yadda aka zata ba, don har yanzu akwai gidajen ‘yar gagara da yawa a Kano da mashayar giya da masu tallar magani suna batsa.
Al’umma na da tambayoyi wanda ko dokar ta iya amsa su:
I. Shin idan mai kuxi ya qara aure sai kuma ya talauce ya za ai da shi?
II. Kuma shin waye talaka ko kuma da wanne ma’auni za a gane talaka?
III. Idan talaka ya je ya karo aure a wata jihar ya za ai da shi?
IV. Shin matan da suka yi kwantai ya za ai da su? Wanda yanzu ma muna da ‘yan mata ‘yan shekaru 30 zuwa sama, da yawa ba mijin aure.
A qarshe gaskiya ya kamata a duba wannan batu don akwai hanyoyin da dama da za a bi da suka fi kafa dokar da ba dole ba ne ta yi aiki. Misali. wa’azi da shirye-shirye (Programs) a kafafen yaxa labarai da wasan kwaikwayo da waqoqi da sauransu. Saboda mafiya yawan masu aikata hakan akwai jahilci a tattare da su, ko dai na ilmin shari’a ko kuma na zamantakewa.
Ina fatan za a duba lamarin da idon basira, don kada a yi gyaran gangar auzunawa.
Za a iya tuntuvar Malam Tijjani ne a [email protected]