Tsohon Shugaban Majalisar Dattijai Abubakar Bukola Saraki ya ce batun da Gwamnan Kwara Abdurrahman Abdulrazaq ya yi cewa ya yi amfani da matsayinsa a baya ya hana EFCC aikinta kazafi ne.
Gwamnan ya zargi Saraki da amfani da matsayinsa na shugaban majalisa na wancan lokacin, don hana EFCC binciken almundahanar da ya yi a Hukumar Ilimi Na Bai Daya (UBEC).
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 4 bayan karbar kudin fansa a Taraba
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 4 bayan karbar kudin fansa a Taraba
Sarakin ya bai wa gwamnan sati daya ya janye kalamai na sa, ko kuma ya amsa kira a kotu.
“Ina ta kau da kai kan kazafin da yake yi min na tsawon lokaci, saboda na san yana yi ne don kau da hankalin mutane daga gazawar gwamnatinsa.
“Amma yanzu zan dau matakin kai shi kotu, tunda bai san zuru ba.
“Don haka na bawa lauyoyina umarnin rubuta masa takaradar gargadin ya janye kalamansa ko na maka shi a gaban kotu”, in ji Saraki.