Wani mutum mai suna K Praveen, mai shekara 21 daga birnin Thiruthangal na Gundumar Birudhunagar a Jihar Tamil Nadu da ke kasar Indiya, ya zamo wanda ya fi kowa tsawon harce a duniya inda aka tabbatar yana da harce mai tsawon santimita 10.8, kamar yadda Littafin Kundin Tarihi na Indiya ya sanar.
A cewar Jami’ar Edinburgh, matsakaicin harcen namiji yana kusa da tsawon santimita 8.5 ne, wanda ya sa harcen K Praveen ya dara haka da tsawon santimita 2.5, kuma mai yiwuwa shi ne ma fi tsawo a duniya.
Wannan matashin dalibi ne a fannin fasahar kere-kere na mutum-mutumi (robotics), kuma ya san cewa, harcensa ya wuce yadda aka saba gani, tun lokacin da ya fara nuna wa abokansa da ’yan uwa abin da zai iya yi da shi.
Matashin yakan yi amfani da harcen yana taba kofar hancinsa da gwiwarsa, kuma yana iya kusan taba idanunsa da harcen.
- ’Yan bindiga sun kashe fiye da mutum 50 a Zamfara
- Rubutu da karatun Hausa na ganin tasku a zamanin yau
Saboda rashin kudi, bai samu damar auna harcen a hukumance ta hanyar samun lambar Kundin Tarihi na Duniya na Guinness Records ba, amma sunansa ya samu shiga cikin littafin tarihi na kasar Indiya na Limca Book of Records, saboda ya kasance mafi tsawon harce a kasar.
Kundin Tarihi na Guinness Record ya ce harce mafi tsawo a duniya a halin yanzu shi ne Nick Stoeberl, da ke birnin Salinas a Jihar Kalifoniya ta Amurka, mai tsawon santimita 10.1 a hukumance. Wannan ya gaza na K Praveen da santimita 0.8.
A yanzu haka dalibin dan Indiya yana shirin tara kudi don tuntubar Kungiyar Shiga Kundin Tarihi ta Duniya, kuma ya yarda harcensa a hukumance ya fi na kowane mutum tsawo.
Praveen, ya ce “Duk da cewa an rubuta nasarorin da na samu a tarihin Indiya, ina neman sunana ya daukaka a duk duniya.
“Wannan zai yiwu idan Gwamnatin Jihar Tamil Nadu ta ba ni tallafi, tun da ba zan iya nuna nasarorin da na samu a duniya ba, saboda rashin kudi.”
A yanzu haka dalibin yana kokarin yadda harcen zai iya taba fatar idanunsa, lamarin da yake ganin zai inganta masa damar samun sa sunansa a cikin littafin Kundin Tarihi na Guinness Book of Records.