Magoya bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar Jamhuriyar Nijar sun gudanar da tattaki gami da wake-wake a harabar majalisar dokokin kasar da ke birnin Yamai.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa duk da mamakon ruwan saman da aka wayi gari da shi a birnin Yamai, magoya bayan juyin mulkin dauke da tutocin kasar Rasha, sun rika cashewa da wakokin goyon bayan sojoji a harabar majalisar.
- Juyin Mulkin Nijar: Ministan Bazoum ya nada kansa Shugaban Gwamnati
- Yadda Zakkar dukiyar Dangote da BUA za ta rage talauci a Arewa
Sun kuma rika sukar Faransa, wadda ta yi wa kasarsu mulkin mallaka, lamarin da ake gani a matsayin karin dakushewar farin jinin Faransa a yankin Sahel, inda Rasha take kara kama kasa.
Tuni da ma dangantaka da Rasha ta yi karfi sosai a kasashen makwabatan Nijar a yankin Sahel da sojoji suka yi juyin mulki, irin su Mali and Burkina Faso, inda suka raba gari da kasashen Turai.
Tun bayan da dangantakar kasashen Turai ta yi tsami da Mali da Burkina Faso, turawan suka fara janye dakarunsu daga yankin, lamarin da ya sa kasashen Taran suka kulla alakar kut-da-kut da Nijar wajen yakar masu tayar da kayar baya.
A bara ne Farasan ta girke dakarunta a kasar Nijar, bayan da ta janye su daga Burkina Faso.
Bazoum ya yi kira a bijire wa sojoji
A safiyar Alhamis kungiyar Tarayyar Afirka da kasar Jamus suka bukaci sojojin su saki Bazoum, bayan da suka bi sahun kasashe da hukumomin duniya da suka la’anci juyin mulkin.
Hambararren shugaban, ya yi kira ga masoya dimokuradiyya a kasar su bijire wa juyin mulkin da sojoji suka yi wa gwamnatinsa.
A sakon da aka fitar ta shafinsa Bazoum na sada zumunta ranar Alhamis, ya lashi takobin kare nasarar dimokuradiyya da kasar ta samu “da jibin goshi”.
Tuni da ma ministan harkokin wajen kasar, Hassoumi Massoudou, ya shaida wa kafar yada labaran Faransa cewa har yanzu gwamnatin Bazoum ce halastaciyyar hukuma a kasar ba ta masu juyin mulki ba.
A cewarsa Bazoum yana cikon koshin lafiya a hannun sojojojin da ke tsare da shi, inda ya ce ba daukacin rundunar sojin kasar ba ne ko goyon bayan kifar da gwamnatin.
Kamfanin dillancin Labaran Faransa (AFP) ya kuma ruwaito ministan yana ayyana kansa a matsayin shugaban gwamnatin kasar.
Rundunar Sojin kasa ta goyi bayan juyin mulki
Bayan sakon na Bazoum ne rundunar sojin kasar ta bayyana goyon bayanta ga juyin mulkin da dakarunta sojin kasar suka yi wa shugaban.
Majalisar sojin ta sanar da hakan ne a ranar Alhamis, tana mai cewa abin da suka sa a gaba shi ne kawar da yamutsi a kasar da dakarun rundunar da ke gadin shugaban kasar suka yi wa Mista Bazoum.
“Ya zama wajibi mu kare martabar shugaban kasa da iyalansa, da kuma kawar da duk wani rikici da ke iya kai ga zubar da jini ko tabarbarewar tsaron al’ummar kasa”, in ji sanarwar da sojojin suka fitar.
Birnin Yamai dai ya kasance tsit a ranar Alhamis, inda aka wayi gari da mamakon ruwan sama gami da matakan takaita zirga-zirga da rufe iyakokin kasar da sojoin suka yi a kasar, wadda ke da alakar mai karfi da kasashen yammacin wajen yakar ta’addanci a yankin Sahel.
Kasashen Yammacin duniya dai sun ce kawo yanzu dai ba kai gano takamaiman manufar sojojin da suka yi wa Bazoum juyin mulki ba.
Abin da masu juyin mulkin Nijar suka yi
A wata sanarwar talabijin da sojojin suka yi cikin tsakar dare, sun sanar da sauke Mista Bazoum daga matsayinsa na shugaban kasa da kuma jingine kundin tsarin mulkin kasar.
Sun kuma sanya dokar hana zirga-zirga daga karfe 10 na dare zuwa 7 na safe, gami da rufe iyakokin kasar da kuma kiran kasashen waje da kada su tsoma baki a kan lamarin da ke faruwa a kasar.
Juyin mulki na bakwai ke nan da aka yi a yankin Yammaci da Tsakiyar Afirka a shekaru uku da suka gabata.
Juyin mulkin da aka yi wa Bazoum ya samo asali ne bayan da aka wayi garin Laraba da sojoji sun tsare shugaban a cikin fadar gwamnati, inda suka hana shiga da fita daga fadar gwamnatin.
Daga baya magoya bayan shugaban suka yi zanga-zanga zuwa fadar gwamnatin, amma sojojin da suka yi garkuwa da shi suka tarwatsa su.