✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Zakkar dukiyar Dangote da BUA za ta rage talauci a Arewa

Zakkar dukiyarsu ta isa a raba wa mutum 437,000 Naira miliyan daya kowannensu

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, da abokinsa, Abdulsamad Rabi’u, Shugaban Rukunin Kamfanonin BUA, su ne suka fi kowa arziki a Najeriya, kamar yadda rahoton kafar yada labarai ta Forbes na jerin manyan attajiran duniya na 2023 ya nuna.

Dangote da Abdulsamad ’yasan asalin Jihar Kano da ke Arewacin Najeriya ne, kuma yankin ne ya fi fama da talauci a kasar mai yawan al’umma miliyan 223.8.

Shin wane irin alfanu za a iya samu a wajen rage talauci, da za a yi amfani da zakkar dukiyar wadannan Kanawa biyu a jiharsu ko yankin Arewa ko ma kasar baki daya.

Dukiyar Aliko da Abdulsamad, wadanda cibiyar kasuwancin kowannensu ke yankin Kudanci, ta haura jimillar abin da attajirai takwas mafiya arziki a yankin na Kudu suka mallaka.

Dukiyar Dangote da Abdulsamad

Hasali ma, jimillar dukiyar tasu ta Naira tiriliyan 17.5 (Dala biliyan biliyan 22.1), ta kusan kasafin kudin kasar na 2023 (Naira tiriliyan 20.5).

Dangote mai matatar mai da masana’antar siminti mafiya girma a Afirka da kuma masana’antar motoci da ta kayan masarufi — sukari, gishiri, sunadarin dandano, taliya — ya mallaki Naira tiriliyan 11.2 (Dala biliyan 14.2), wanda ya zarce rabin kasafin kudin Najeriya na 2023 na tiriliyan 20.5.

Shi kuwa Abdulsamad Rabiu mai kamfanin BUA masu siminti da shinkafa da sukari da taliya, yana da Naira tiriliyan 6.3 (Dala biliyan 7.9), kimanin rabin abin da Dangote ya mallaka.

Idan aka raba dukiyarsu…

Da za a raba dukiyar Dangote da Abdulsamad Rabiu wa daukacin talakawan Najeriya, mutum miliyan 133, kowannensu zai samu Naira 131,579.

Muna kawo wannan misali ne domin nuna yawan arzikin da Allah Ya yi wada wadannan talikan nasa, amma babu hikima a ce a rabe dukiyarsu gaba daya, karshenta a yi haihuwar guzuma.

A matsayinsu na Musulmi ma, zakka ce ta wajaba a cire a cikin dukiyar tasu, wadda da za a yi wa talakawan kasar kudin goro, manya da kanana, kowannensu zai su samu N3,289.5 — wanda ba zai taka kara ya karya ba.

Da kuma za a takaita rabon zuwa ga mutum miliyan 71 da suke cikin matsancin talauci a kasar, duk uwar darin ce, domin bai wuci su samu N6,161, kowannensu ba.

Da yake daga jihar Kano mai mutum kusan miliyan 20 Dangote da Abdulsamad suka fito, da za a sarrafa zakkar tasu, kowa zai tashi da Naira 109,395, idan aka takaita zuwa ga talakawan jihar mutum miliyan 3.96 kuma (wadanda su ne kashi 90 na al’ummar jihar), za su samu N110,479 kowannensu.

Amma da za a sarrafa zakkar dukiyar domin tallafa wa masu kananan sana’o’i, watakila su ja jari domin nan gaba su ya tsaya da kafarsu, zakkar ta isa a ba wa mutum 437,500 Naira miliyan daya kowannensu.

Daga zakkar Dangote ta Naira biliyan 280, mutum 280,000 za su iya samun Naira miliyan Daya kowannensu. Zakkar Abdulsamad ta Naira miliyan 157.5 kuma, za a iya ba wa mutun 157,500 miliyan guda kowannensu.

Da za a raba wa ’yan kasar Naira dubu takwas da gwamnati ta yi wa mutum miliyan 12 alkawari bayan janye tallafin mai kuwa, mutum …. ne za su amfana na tsawon wata shida.