Kungiyar nan mai rajin kare hakkin Musulmai ta MURIC, ta shawarci sojojin Najeriya da kada su kuskura su yi koyi da takwarorinsu na Gabon wajen yin juyin mulki.
Da sanyin safiyar Laraba ce dai sojojin kasar ta Gabon suka sanar da juyin mulkin da ba a zubar da jini ba bayan sun kifar da gwamnatin Shugaban Kasa, Ali Bongo.
- ‘Tinubu na maimaita kura-kuran Buhari a fannin tattalin arziki’
- Tinubu ya damu matuka da halin da ake ciki a Gabon – Ngelale
Shugaban kungiyar ta MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ne ya bayar da shawarar a cikin wata sanarwa ranar Laraba.
Sanarwar ta ce, “Duk da ba ma jin dadin salon da iyalan Bongo suke bi wajen shugabantar kasar Gabon da ma wasu kasashen Afirka, amma muna alla-wadai da wannan juyin mulkin.
“MURIC na shawartar sojojin Najeriya da su ci gaba da nesanta kansu daga siyasa, sannan su yi watsi da yunkurin zuga su domin su kitsa juyin mulki a Najeriya.
“Duk sojan Najeriya da ya yi tunanin yin juyin mulki a halin da ake ciki yana yin haka ne saboda son zuciyarsa. Ya kamata a lura da cewa tsarin siyasar Najeriya ya sha bamban da irin na kasar Gabon, wanda ’yan gida daya ke ta mulki har sama da shekara 50.
“Duk wani yunkuri na yin juyin mulki a kan wannan mulkin na Musulmai biyu, za mu dauke shi a matsayin kai hari a kan Musulmai, la’akari da irin tirka-tirkar da aka sha kan tsayar da Musulmai biyu a zabe.
“Juyin mulki a Najeriya a yanzu zai daukifassarar addini. Har yanzu Najeriya ba ta warke daga juyin mulkin da aka yi wa ’yan Arewa ba a ranar 15 ga watan Janairun 1966 wanda sojoji ’yan kabilar Ibo suka aiwatar a kan sojojin Arewa.”
Ya ce sojojin Najeriya na da kwarewa sosai, kuma ’yan Najeriya na alfahari da su saboda kwarewar tasu.
Farfesa Ishaq ya kuma ce yanzu haka ma sojojin na Najeriya na fama da rikice-rikice irin na ta’addanci da sauran rigingimu da bai kamata su kara da na siyasa ba.