Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da ayyukanta na agaji a Jamhuriyar Nijar, sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi wa shugaban kasa Mohamed Bazoum.
A yayin da mutum sama da miliyan hudu da ke tsananin bukatar agaji a kasar, Sakataren Majalisar, Antonio Guterres ya bukaci sojoijn su saki Shugaba Bazoum da ke tsare a hannunsu ba tare da bata lokaci ba.
- Ministoci: Dalilin da Tinubu bai ba da suna daga Kano ba
- Ministocin Tinubu: Babu Kano, Adamawa, Lagos
A safiyar Juma’ar ce dai Ministan Harkokin Wajen Faransa, ya ce Mista Bazoum ya tattauna da Shugaba Emmanuel Macron kuma yana cikin koshin lafiya.
A bangare guda kuma, an haramta zanga-zanga gaba daya a Nijar bayan harin da wasu masu zanga-zanga suka kai hedikwatar Jam’iyyar PNDS Tarayya ta Shugaba Bazoum da aka kifar da gwamnatinsa.
Ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta umarci jami’an tsaro su kare dukiyar kasa, da cewa, “Daga yanzu an haramta kowane irin zanga-zanga kuma za a hukunta duk wanda ya saba wannan umarni,” domin gwamnati ba za ta hukunci lalata dukiyar kasa ba.
Yadda aka kona hedikwatar jam’iyya mai mulki
Washegarin juyin mulkin ne dai magoya bayan juyin mulki dauke da tutocin Nijar da Rasha suka kai gami da kone-kone a hedikwatar Jam’iyyar PNDS Tarayya ta hambararren Shugaban Kasa Mohamed Bazoum.
An kai harin ne a yayin da Bazoum ke nuna turjiya, inda ministansa na harkokin waje, Hassoumi Massoudou, ya ayyana kansa a matsayin shugaban gwamnati.
Masu tarzomar wani yanki ne na magoya bayan juyin mulkin, wadanda suka je harabar majalisar dokokin kasar — wasunsu dauke da tutar kasar Rasha — a ranar Alhamis, domin jaddada goyon bayansu sojojin.
Dakararun tsaron fadar shugaban kasar ne suka yi juyin mulkin, kuma yanzu rundunar sojojin kasar ta mara musu baya.
Tun bayan kifar da gwamantin Bazoum a ranar Laraba, sojojin suke tsare da shi, duk da cewa Majalisar Dinkin Duniya da Rasha da sauran kasashen duniya, sun bukaci sojojin su sako shi ba tare da bata lokaci ba.
Ta’addanci a Nijar
Bazoum wanda aka rantsar bayan cin zabe a shekarar 2021, ya kasance babban abokin kawancen kasashen yammacin duniya wajen yaki da ta’addanci a yankin Sahel.
Kasashen Amurka da Faransa, wadda ta yi wa kasar mulkin mallaka sun kafa sansanin sojoji a kasarsa, sakamakon hakan.
Matalauciyar kasar tana fama da ta’addancin masu ikirarin jihadi a yankunan da ta yi iyaka da kasashen Mali da kuma Najeriya.
Wannan matsala dai ta yi kamari a yankin Sahel da ma Najeriya, wadanda suka kulla kawance wajen yakar ta.
Mali da Burkina Faso sun raba gari da Faransa
Sai dai a baya-bayan nan, Mali da Burkina Faso, inda sojoji suka yi juyin mulki, sun raba gari da Faransa tsohuwar uwargijiyarsu wadda ta girke dakarunta a kasashensu domin yakar ’yan ta’addan.
Kasashen biyu sun zargi Faransa da mara wa ’yan ta’ddan baya, har suka umarci sojojinta su fice daga kasashensu, inda suka kulla kawance da Rasha, wajen sayen makamai, domin yakar ’yan ta’ddan.
Sojojin kasar na ikirarin samun kyakkyawan sakamako bayan kawancen da suka kulla da Rasha, wadda a hlin yanzu sojojin hayanta na Wagner Group suke taimaka musu a wannan aiki.
Siyasar Amurka, Faransa da Rasha a Sahel
A baya-bayan nan Faransa ta girke sojojinta da ta kwaso a kasar Nijar, bayan sojojin da ke jan ragamar mulkin kasar Mali sun kore su.
Faransa da Amurka dai ba sa ga maciji da Rasha, wadda wasu ke ganin za ta iya samun gindin zama a Nijar, muddin sojojin da suka yi juyin mulki za su yi koyi da takwarorinsu na Mali da Burkin Faso.