✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jos ta Arewa: Kotun Daukaka kara ta soke zaben Hon. Agah

Kotun daukaka karar ta tabbatar da Muhammad Adam Alkali na Jam'iyyar PRP a matsayin zababben dan Majalisar Tarayyar mai wakiltar mazabar.

Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin soke zaben dan Majalisar Tarayya na Jos ta Arewa/Bassa, Musa Avia Agah na Jam’iyyar PDP, tare da sauke shi daga kujerarsa.
Kotun daukaka karar ta kuma tabbatar da dan takarar Jam’iyyar PRP, Muhammad Adam Alkali a matsayin zababben dan Majalisar Tarayyar mai wakiltar mazabar.

Kotun daukaka karar sanar da haka ne bayan ta yi watsi da karar da Honorabul Musa Avia Agah ya daukaka zuwa gabanta yana kalubalantar hukuncin kotun kararrakin zabe da ta soke zabensa a tun ranar 2 ga watan Satumba.

Kotun ta umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana Muhammad Adam Alkali na PRP a matsayin wanda ya lashe zaben sannan ta mika masa takardar shaidar cin zaben mazabar.

Hon Agah ya daukaka kara zuwa kotun ne yana neman so ta yanke hukunci ko kotun baya ta yi daidai wajen cewa ba a yi zaben sa a matsayin dan takara ta halasciyar ba, sannan ko ya dace a ayyana Alkali a matsayin wanda ya ci zabe.

Amma a hukuncin na ranar Juma’a, alkalan kotun, Masu Shari’a Tani Y. Hassan, A. I. Andeyangtso da kuma J.G. Abundaga, sun yi ittifakin kotun bayan ta yi daidai.

Ta bayyana cewa jam’iyyar PDP ta saba umarnin Babbar Kotun Jihar Filato na gudanar da babban taronta, don haka ba ta cika sharadin tsayar da dan takara ba.