Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya mayar wa tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo da martani a game da wasikar gazawar shugabanci da ya rubuta masa ranar 2 ga Disamba, inda a cikin wasikar Jonathan ya kare kansa tare da musanta zarge-zargen da Obasanjo ya yi masa.
Shugaba Jonathan dai ya rubuta wa Obasanjo martanin ne a ranar 20 ga watan Disambar nan, mai yawan shafuka 16, kuma shugaban ya zana dililai guda 10 da ya ce suka sanya ya zama wajibi ya mayar wa tsohon shugaban da martani.
A cikin wasikar, Jonathan ya bayyana irin rawar da Obasanjo ya taka a lokacin yakin neman zabensa, tare da bayyana wasikar Obasanjo a matsayin babbar barazana ga sha’anin tsaron kasa.
Jonathan ya bayyana Obasanjo da cewa mutum ne mai muhimmin matsayi a Najeriya, domin ko ba komai ya mulki kasar nan a zamanin mulkin Soja da kuma lokacin dimokuradiyya har na tsawon shekara 11 da wata 8.
Jonathan ya ci gaba da cewa ya zama wajibi a gare shi ya mayar wa tsohon shugaban kasar da martani saboda Obasanjo ya bai wa duniya damar sanin abin da ke cikin wasikarsa a daidai lokacin da shugabann majalisar wakilai ta tarayya shi ma yake zargin gwamnatinsa da gazawa wajen yaki da rashawa da ta yi wa kasar nan katutu, yayin da shi kuma gwamnan babban bankin kasar nan shi ma ya fito yana zargin kamfanin mai na kasa (NNPC) da kin zuba wa asusun tarayya kudi fiye da dala biliyan 48, abin da Jonathan yake ganin tamkar hadin baki ne a tsakanin wadannan mutane.
A game da batun matsalar tsaro, musamman ma rikicin Boko Haram, Jonathan a martanin nasa ya nuna cewa, matsalar ta samo asali ne tun a shekarar 2002, inda yace yana daukar matakai da kuma samar wa jami’an tsaro kayan aiki domin shawo kan matsalar.
Jonathan ya kuma karyata zargin da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yi na cewa gwamnatinsa ta tsara sunayen wadansu mutane guda dubu a fagen siyasa da nufin halaka su, yana mai cewa a tarihin Najeriya an san gwamnatocin da suka saba kashe ‘yan hamayya, amma ba gwamnatin Jonathan ba.
A game da batun yaki da rashawa kuwa, Jonathan ya maryar wa Obasanjo da martani ne da wadansu baitoci a cikin wakokin da Fela ya rera masa (Obasanjo) a zamanin mulkinsa.
Shugaba Jonathan wanda a cikin wasikarsa tasa ya rika kiran Obasanjo da sunan Baba, ya ce ya bayar da umurnin a gudanar da bincike a kan jerin zarge-zargen da Obasanjo ya yin a cewa gwamnatinsa na horar da ‘yan ina-da-kisa a wani wuri da tsohon shugaban kasa marigayi Janar Sani Abacha ya horar da nasa.
Jonathan ya ce, ‘’Baba, ban san daga ina ka samo wannan bayanin ba, sai dai ba ka kyauta mini dab a ka bayyana hujjarka game da wannan zargin ba, amma ka bayyana wa duniya. Ka ambaci sunan Allah sau goma sha bakwai a cikin wasikarka, ko a matsayinka na kirista za ka rike Bible ka ce lallai wannan abin da ka fada ka yi imani gaskiya ne?’’
Dangane da batun Boko Haram kuwa, Jonathan cewa ya yi matsalar ta samo asali ne a lokacin mulkin Obasanjo, kuma a halin yanzu gwamnatinsa tana iyakar kokarinta wajen magance matsalar.’’ An rikicin Boko Haram ya faro ne daga shekara 2002, ba Goodluck Jonathan ne ke shugabancin kasar ba a lokacin. Haka kuma matsalar fashi da makami ta yi kamari ne bayan kamala yakin basasa a kasar nan kuma tun daga lokacin ta ci gaba da ci wa kowace gwamnati tuwo a kwarya, domin haka idan aka samu wani tsohon shugaban kasa day a kamata a ce san haka amma ya fito ya nuna kamar gwamnatin Jonathan c eta haifar da wannan matsalar, lallai abin takaici ne.’’
‘’ za a yi mamakin yadda yanzu ka koma mai ra’ayin cizawa da hurawa a game da matsalar Boko Haram, musamman idan aka yi la’akari da yadda ka murtsuke garin Odi a jihar Bayelsa domin murkushe masu tayar da kayar baya a yankin Neja delta. Idan murkushe garin Odi da sojoji suka yi shi ne cizawa, ai ba mu ga kuma inda aka hura ba. A lokacin da aka aikata haka ina rike da mukamin mataimakin gwamna ne a jihar, kuma na sha fada maka cewa mamaye garin Odi da aka bai amfanar da komi ba wajen rage masu tayar da kayar baya a yankin, hasali ma dai maimakon raguwa sai karuwa matsalar ta yi.’’
A kan batun cin hanci da rashawa kuwa, Jonathan cewa ya yi matsalar ta faro ne shekaru da yawa da suka gabata, kuma hatta a lokacin gwamnatin Obasanjo ana sane da badakalar kamfanonin Siemens da Haliburton.’’
A martanin da Jonathan ya aika wa Obasanjo ya bayyana irin matakan da gwamnatinsa ta dauka wajen magance matsalar tsaro, da suka hada da sake wa rundunar ‘yan sandan kasar nan fasali dab a su isasshen kudi tare da horar das u da kuma wadata su da ababen hawa. Haka kuma jami’an Cibil defence su ma an karfafa su ta hanyar ba su bingpogi yadda za su iya agaza wa ‘yan sanda.
Ya kuma nuna cewa, gwamnatinsa ta himmatu wajen magance matsalar satar danyen mai, inda ta hada kai da gwamnonin jihohi, kuma ta nemi taimakon gwamnatocin Amurka da Ingila domin a kwato kudin da aka sayar da man da aka sata.
Haka kuma Jonathan ya bayyana a cikin martanin da ya aika wa Obasanjo cewa, tsohon shugaban kasa Obasanjo ne yake kokarin haifar da kiyayya a tsakanin mambobin Jam’iyyarsa ta PDP, sabanin yadda shi Obasanjon ya nuna a wasikarsa cewa take-taken Jonathan ne suke haifar da baraka a jam’iyyar PDP din. ‘’Abin takaici ne day a kasance wadansu ‘yan tsirarun jiga-jigan jam’iyyar PDP ne suke rura wutar fitina a jam’iyyar, kuma kana cikinsu.’’
A karshen martanin da Jonathan ya tura wa Obasanjo, Jonathan cewa ya yi, ‘’ Ina so in bayyana maka cewa ba ka yi mini adalci ba da ka zarge ni a cikin budaddiyar wasikarka da cewa ni mayaudari ne, makaryaci, mazambaci, kasasshe, mai nuna bambancin kabilanci, da sauran munanan abubuwa.’’
‘’Ni ban taba cewa ni gwani ne ba wanda bay a yin kuskure ba, amma kuma ban taba yawo da hankalin ‘yan Najeriya ba kamar yadda ka nuna, kuma zan ci gaba da yin iyakar kokarina wajen ganin an kai Najeriya tudun-mun-tsira kamar yadda dukkanmu muke fata.’’
Ba zan amsa wa Jonathan ba -Obasanjo
Sai dai kuma shi tsohon shugaban kasa Obasanjo ya bayyana cewa ba zai mayar da martani ga amsar da Jonathan ya ba shi ba.
A wata sanarwa da kakakin Obasanjo Tunde Oladunjoye ya raba wa manema labarai a Abeokuta, an nuna cewa tsohon shugaban kasa Obasanjo ba zai sake yin wata magaba dangane da wannan amsa da Jonathan ya tura masa, domin kuwa a bayanin da Obasanjon ya yi babu wani abu da ke bukatar karin bayani.
A cewar sanarwar, ‘’an yi ta kiraye-kiraye a kafofin yada labarai na ciki da wajen kasar nan ana son a ji abin da Obasanjo zai ce game da shugaban kasa ya ba shi. To, Cif Olusegun Obasanjo dai ya karbi martanin da aka aika masa, sai dai kuma kamar yadda ya riga ya bayyana a wasikarsa day a aika wa shugaba Jonathan a ranar 2 ga watan Disamba 2013, bay a bukatar sake yin wata Magana bayan bayanin day a yi a wasikar tasa.’’
Sanarwar ta yanko wani sashe a shafi na 14 sakin layi na biyu na wasikar da Obasanjo ya aika Jonathan inda yake cewa, ‘’ wannan wasika da na rubuta maka na yi abin day a kamata in yi maka, kamar yadda na saba yi wa gwamnatinka da jam’iyyar PDP da kuma kasarmu Najeriya.’’
Sanarwar ta ci gaba da jaddada cewa, Cif Olusegun Obasanjo yana manukar girmama ofishin shugaban tarayyar Najeriya.’’