✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jonathan na amfani da sojoji ta hanyar da ba ta kamata ba – Sanata Goje

Sanata Muhammad danjuma Goje (APC, Gombe) shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Harkokin Man Fetur (Gangaren Teku) daya daga cikin kwamitocin da alhakin kafa dokar harkokin…

Sanata Muhammad danjuma Goje (APC, Gombe) shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Harkokin Man Fetur (Gangaren Teku) daya daga cikin kwamitocin da alhakin kafa dokar harkokin man fetur (PIB) da ake takaddama a kanta ke wuyansu. A wannan tattaunawa Goje ya zargi Ma’aikatar Man Fetur da Kamfanin NNPC da kuma Gwamnatin Tarayya kan jan kafa game da amincewa da dokar. Kuma ya nuna damuwa kan yadda Shugaba Goodluck Jonathan ke neman zama dan kama-karya:

Yaya za kwatanta shekara ukunka a Majalisar Dokoki?
 Zamata a Majalisar Dattawa a shekara uku ya ba ni damar kara gogewa, a yanzu na fahimci wasu abubuwa ta wani gefe daban. Na taba zama dan majalisar jiha a Jamhuriyya ta Biyu, wanda ya bambanta da wannan. Gogewar da na samu a Majalisar Dattawa ya sha bamban, kuma za ka iya samunsa haka ne kawai idan ka shiga cikinta. Duk yadda wani ya rika yi maka bayani ba za ka iya gane hakikanin majalisar ba sai ka zauna a cikinta. Na fahimci abubuwa da dama a shekara ukun da suka gabata.
Yaya za ka bayyana yadda Majalisar Dattawa ta gudanar da ayyukanta a shekara uku da suka gabaata?
Ina ganin Majalisar Dattawa ta yi bakin kokarinta a shekara uku da suka gabata ta wajen amincewa da kudirori da dokoki da shawarwari kan al’amura da dama, sai sanya ido da tsoma baki da bayar da shawarwari a al’amura da dama. Gaba daya Majalisar Dattawa ta yi iyaka kokarinta duk da dimbin kalubalen da ke akwai da kuma yadda ’yan Najeriya ke kallonmu.
 ’Yan Najeriya da dama suna kallon Majalisar Datttawa a matsayin ’yar amshin shatar bangaren zartarwa ce, saboda kullum ana ganin ba ku daukar mataki masu kaushi kan al’amura masu muhimmanci, me ya sa haka ke faruwa?
Kuskure ne a ce koyaushe muna goyon bayan bangaren zartarwa. Bambancin da ke akwai shi ne wasu daga cikin ayyukan da muke yi, Majalisar Wakilai ba ta yi. Sun hada da wanke ministoci ko mukamai da dama da tsarin mulki ya nema. Idan bangaren zartarwa ya zabi wadanda za a nada kan mukamai, in muka samu sun cancanta kuma sun dace babu dalilin da za mu ki amincewa da su. Don haka Majalisar Dattawa tana daukar matakai da dama da suka saba wa bangaren zartarwa, misali dauki batun kara kudin man fetur da sunan janye tallafi mun yi magana. kudiri na farko kan janye tallafin mai da Sanata Bukola Saraki ya gabatar a shekarar 2011 ne ya zama sa ka dan ba kan lamarin. Sannan batun hukumar kasuwar zuba jari mun dauki matakin da ya saba da na bangaren zartarwa. Akwai matakai da dama irinsu da ba zan iya fadinsu a nan ba. To amma saboda yawan mukaman da muka amince da su wadanda sun kebanta ga Majalisar Dattawa ne, ya sa ake yi mana gurguwar fahimta a dauka muna tare da bangaren zartarwa ne.
Gwamnatin Tarayya tana daukar wasu matakai da mutane da dama ke ganin na musgunawa da kama-karya ne, me za ka ce kan haka?
Abin takaici ne kuma babban abin damuwa a ga muna komawa ga mulkin kama-karya a baya-bayan nan, ni kaina lamarin ya shafe ni kwanan nan a Kano, inda aka hana hana jirginmu tashi ba bisa doka ba. An tilasta mu barin Kano a cikin dare ta sufuri a cikin mota inda muka iso Abuja da karfe 2:30 na dare ba tare da mun yi  wani laifi ba, kuma a cikinmu har da gwamna mai cid a sanatoci biyu da tsofaffin gwamnoni da tsohon shugaban Jam’iyyar PDP. Kuma irin haka ya faru a Jihar Ekiti, inda aka hana gwamnoni shiga jihar. Irin wadannan abubuwa bai kamata su rika faruwa a lokaci na dimokuradiyya ba. Sannan kai farmaki ga gidajewn jaridu yana kara ta’azzara a wannan lokaci na gwamnatin Jonathan. Kuma wadannan duk suna faruwa ne a daidai lokacin da ake tunkarar zaben 2015. To idan wadannan abubuwa na faruwa yanzu, Allah ne kawai Ya san abin da zai faru a badi. Idan sojoji suka ci gaba da musguna wa abokan adawa, to ya zamo babu dimokuradiyya ke nan, bai kamata a rika amfani da sojoji kamar haka ba. Kamata ya yi su bayar da damar da ta dace ga dukkan ’yan kasa, amma ba su rika fifita bukatun siyasa na Jam’iyyar PDP da Gwamnatin Tarayya ba.  
Me wannan ke nunawa ga dimokuradiyyarmu?  
Ba ya nuna alheri, amma muna fata bisa yadda kukan da jama’a ke yi, Jam’iyyar APC ta dauki matsayar kai Gwamnatin Tarayya kotu kana bin da ya faru a Ekiti musamman hana mutane damar kai-kawo a ko’ina a cikin kasar nan kamar yadda tsarin mulki ya tanada. Hana shiga da fita Jihar Ekiti kacokan kafin zabe abu ne da ba a taba yi haka a baya ba. Dukkan ’yan Najeriya da suka damu da dorewar dimokuradiyya sun fito fili sun yi Allah wadai da gwamnati, kuma sun nemi ta daina amfani da jami’an tsaro ta hanyar da ba ta kamata ba.
Kana dora laifin haka ne kan Shugaban kasa?
Ba na son alakanta lamarin da wani mutum, amma ina ganin hakan a matsayin wani yunkuri na wani rukunin mutane da suka kagara su dora kansu a mulkin jama’a ta amfani da Jonathan.
To amma alhakin yana wuyansa a matsayinsa na Shugaban kasa…
Na sani, kuma ba ina wanke shi ba ne. A matsayinsa na Shugaban kasa yana da cikakken iko nay a hana komai, ya yi watsi ko ya amince ko ya ki amincewa da komai, to amma baya ga shi akwai mutanen da suke kewaye da shi da a cikin jam’iyyarsa da suka makance sai sun ci gaba da mulki ta kowace irin hanya. Kuma wadannan mutane suna taka muguwar rawa wajen tabar da gwamnati tana daukar irin wadannan matakai da ba su dace ba, kuma sun saba wa dimokuradiyya. Ina fata Shugaban kasa a matsayinsa na wanda ya ci gajiyar mulkin dimokuradiyya a shekara 15 da suka gabata, ba zai rusa dimokuradiyyarmu ba.
A matsayinka na Mataimakin Shugaban Kwamitin Man Fetur wane kalubale kwamitinku ke fuskanta?
Na daya, kwamitinmu ba ya samun cikakken hadin kai daga Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur. Kuma wannan babban cikas ne ga aikinmu koda a bangarorin da suke da muhimmanci ga aikinmu, kamar dokar albarkatun man fetur (PIB) wadda ked a matukar muhimmanci ga ingantawa da bunkasa tattalin arzikinmu, amma ba mu samu hadin kan da muke fata ba daga Ma’aikatar Man Fetur  don sanya hannu kan dokar bad a muka aika wa Shugaban kasa. Ba wannan kawai ba, mukan gayyaci jami’ar ma’aikatar da na Kamfanin Mai na kasa (NNPC) wadanda a lokuta da dama ba sa ba mu hadin kai ta wajen amsa gayyatarmu. Kullum sai su rika ba da uzurori. Kuma koda binciken da muke gudanarwa tilas muka dage zaman na dogon lokaci yanzu saboda sun ki ba mu hadin kai. Don haka duk yadda muka kai da haba-haba da karsashin yin aikinmu a matsayinmu na wakilan kwamitin, muna bukatar samun goyon bayan da ya dace daga ma’aikatar domin a cimma wani abu a sanya hannu kan dokar. Hakika mun so mu je wasu kasashen waje mu nazarci dokokin harkokin man fetur dinsu mu gwama mu yi nazari da dokar PIB domin fitar da dokar da ta dace, amma rashin kudi ya hana mu zuwa. Koda a nan cikin kasa mun so mu shirya zaman jin ra’ayin jama’a a kowace shiyya daga cikin shiyyoyin siyasa shida amma rashin kudi ya hana mu, muka kira zaman a zauren majalisa kawai, wannan babbar cikas ne ga kudirin dokar da take da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin kasa. Duk da haka muna bakin kokarinmu, sai dai da za mu yi fiye da haka ida da ma’aikatar ta ba mu hadin kai da goyon baya.
Wane irin hadin kai kake nufi?
Abin da muke cewa, shi ne mun shirya zaman sauraron ra’ayin jama’a, mun sa ran dukkansu su halarci zaman da kansu, amma galibi sukan tura wakilai ne ko ma su ki. Wannan ba abu ne mai kyau ba. Kamata ya yi su kasance a wurin, don mu kadai ba za mu iya amincewa da kudirin ba, ba tare da mun samu shawarwarinsu ba.
Yaushe ’yan Najeriya za su sanya ran a sanya hannu kan dokar albarkatun man (PIB)?
Da yardar Allah za mu sanya mata hannu kafin karshen wa’adin mulkinmu. Mun shirya za mu yi haka. Bilhasli ma mun yi nisa, mun kammala sauraron ra’ayin jama’a, kuma a matakin kwamiti ne a kwamitocin hadin gwiwa hudu. Dukkan kwamitocin suna yin aiki kan sassa da daman a kudirin dokar da suka fado karkashin ikonsu, bayan haka ne za mu mika rahotonmu domin dubawa da amincewa.