Tsohon dan wasan Ingila da Chelsea John Terry ya yi ritaya daga taka kwallon kafa.
John Terry ya yi ritaya ne yana da shekarar 37 a duniya.
A tsawon lokacin da ya dauka yana taka leda, Terry ya bugawa kungiyoyin Chelsea, inda ya fi daukan lokacin sannan kuma tauraronsa ya hasa har aka san shi a duniya, sannan daga bisani ba yar Chelsea bayan ya yi kimanin shekarar 20 a kungiyar ya koma Aston Villa a shekarar 2017.
Terry dai ya sanar da cewa ya bar kungiyar Aston Villa ne a karshen karar bana.
Terry ya buga wa Ingila wasa sau 78, sannan ya lashe gasar firmiyar Ingila sau biyar, da Eurofa sau daya da kuma gasar Zakarun Turai sau daya duk a Chelsea.