Rahotanni da ke fitowa daga Jihar Zamfara sun ce an kashe mutane da dama tare da jikkata wasu a wani hari da sojojin sama suka kai a kauyen Mutunji da ke Karamar Hukumar Maru a ranar Lahadi.
Mazauna yankin sun ce lamarin ya faru ne lokacin da jirgin saman sojoji ya bi wasu ‘yan ta’adda zuwa wata kasuwa a yankin.
- An cafke matashi kan sukar Gwamnan Yobe a kafafen sada zumunta
- An Yi Gwanjon Kayan ’Yan Wasan Netherlands Don Taimaka Wa Ma’aikata Baki A Qatar
A cewar mutanen, sojojin sun yi artabu da ’yan ta’addan na tsawon kwana biyu a unguwar Malele, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa zuwa Mutunji.
Mazauna yankin da lamarin ya shafa sun ce suna cikin kasuwar ne suka ga wani jirgin sama yana yawo, kuma jim kadan sai suka ji kara kamar ta bam.
Saidu Ishaka, daya daga cikin mazauna yankin da ya tsallake rijiya da baya a harin da jirgin ya kai, ya bayyana cewa ya fadi kasa sau biyu saboda girgiza da kasa ta yi kuma yana tashi sai ya ga gawarwaki a ko ina a kasa.
Ya tabbatar da cewa an kai wasu daga cikin wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Kwararru na Yariman Bakura da ke Gusau.
Nuhu Dansadau, mazaunin Masarautar Dansadau, ya ce ‘yan ta’addan sun hada karfi da karfe domin kaddamar da hare-hare a kan al’ummar Malele a lokacin da mazauna yankin suka shaida wa sojoji su kuma suka dakile harin .
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Zamfara, Mammam Tsafe (mai ritaya) wanda ya ziyarci mutanen da suka jikkata a Asibitin Kwararru na jihar, ya yi Allah wadai da kisan, sannan ya bukaci sojoji da su hanzarta kawar da ‘yan ta’addan.
Sojoji sun karyata labarin
Rundunar Sojin Najeriya ta ce babu gaskiya cikin labarin kashe fararen hula a harin da dakarunta suka kai ranar Lahadi a Jihar.
Da yake zantawa da manema labarai, Kwamandan rundunar tsaro ta ‘Operation Hadarin Daji’ Manjo-Janar Uwem Bassey, ya ce babu wani abu mai kama da hakan.
“Lokacin da sojoji ke yakar ‘yan ta’addan, ba a samu wani abu da ya shafi ‘yan kasa ba,” inji shi.
Bassey ya ce an shirya labarin ne don dauke hankulan jama’a daga nasarar da sojoji ke samu a kan ‘yan ta’adda.
“Yawancinsu ‘yan bindiga sun sa sun tsere daga gidajensu. Sun bayyana muku adadin ‘yan bindigar da aka kashe, sun bayyana kasurguman ‘yan ta’addan da aka kawar? Kawai suna son haifar da rudani ne,” inji Bassey.