Fararen hula akalla takwas sun rasu wasu da dama kuma na kwance a asibitoci bayan wani jirgin soji ya yi musu lugugen wuta a kauyen Buhari da ke Karamar Hukumar Yunusari ta Jihar Yobe.
Mazauna kauyen da ke iyaka da Jamhuriyar Nijar sun ce jirgin sojin ya kai musu harin ne a lokacin da suke kokarin fita zuwa cin kasuwa da gonaki da sauran harkokinsu a safiyar Laraba.
Wani mazaunin garin, Ali Lawan, ya ce, “Mutane na cikin rudani game da inda jirgin sojin da ya kai hari ya fito, saboda Boko Haram dai ba da jirgi suka saba kai hari ba.
“Ganin jirgin ya fara luguden wuta sai mutane suka ce kafa me na ci ban baki ba. Amma ya kashe wasu daga cikinsu, wasu kuma ya jikkata su.”.
Ali, wanda ya ce an garzaya da mutum 20, maza da mata da kananan yarao zuwa Babban Asibitin Geidam domin kulawa da su, ya kara da cewa, “Masu munanan raunuka kuma an wuce da su Asibitin Kwararru da ke Damaturu, wasu kuma Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri domin samun kulawa.”
Shugaban Karamar Hukumar Yunusari, Alhaji Bukar Gaji, ya tabbatar wa Aminiya cewa, “Gaskiya ne, mun samu labari yau (Laraba) da safe kuma a halin yanzu wadanda abin ya ritsa da su na samun kulawa a asibiti.
“Ba za mu iya cewa ko jirgin sojin Jamhuriyar Nijar ba ne ko na Najeirya; Sojoji ne kadai za su iya sanin asalinsa,” inji shi.
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Yobe, Dungus Abdulkarim, ya ce jirgin na sojoji ne, saboda haka ba hurumin ’yan sanda ba ne su yi jawabi a kai.
Mun yi kokorin tuntubar kakairin Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya da ke gairn Damaturu, hedikwatar Jihar Yobe, Laftanar Kennedy Anyewau, amma abin ya gagara.
Amma majiyarmu ta soji da ta bukaci a sakaya sunatsa ta tabbatar mana cewa hukumomin sun san da faruwar lamarin.