An shiga fargaba yayin da wani jirgin yaƙi, ya yi wasu ƙauyuka biyu ruwan bama-bamai bisa kuskure a Ƙaramar Hukumar Silame, a Jihar Sakkwato.
Ana zargin gomman mutane, sun rasa rayukansu.
- Yunwa da gazawar gwamnati ne sanadin turmutsutsi wajen rabon abinci — Kukah
- Najeriya ba ta cikin ƙasashen da suka fi cin bashi a Afirka – IMF
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7 na safiyar ranar Laraba, a ƙauyukan Gidan Sama da Rumtuwa.
Wani mazaunin Silame, Malam Yahya, ya bayyana cewa ƙauyukan suna kusa da dajin Surame, wanda ya zama mafakar ’yan ta’adda da Lakurawa.
Wata majiya, ta ruwaito cewa sama da mutum 10 ne suka rasu yayin hare-haren na sama, yayin da wasu da dama suka jikkata.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Silame, Alhaji Abubakar Muhammad Daftarana, ya tabbatar da faruwar harin.
Amma ya ce har yanzu suna aikin tantance adadin asarar da aka yi.
“Mutanen ƙauyen suna zaune lokacin da bama-bamai suka fara sauka.
“Waɗannan mutane suna zaune lafiya ba su da wata alaƙa da laifi.
“A yanzu ba zan iya tabbatar da adadin mutanen da suka rasa rayukansu ko suka ji rauni ba, saboda har yanzu muna aikin tantancewa,” in ji shi.
Lokacin da aka tuntuɓi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ahmad Rufa’i, ya ce zai yi ƙarin haske daga baya.