Wani jirgin soji mallakin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ya hallaka wasu kananan yara shida a wani kauye a Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.
Kananan yaran masu shekaru biyar zuwa 12 sun gamu da ajalinsu ne a wurin da suke dibar ruwa kauyen Kureba, inda jirgin yakin ya yi raga-raga da gidajen jama’a da dama.
- Wani Sauti Mai Karfi Ya Sanya Firgici A Garin Geidam
- Hatsarin jirgin sama 11 da suka kashe hafsoshin sojin Najeriya
- ISWAP ta kai hari Chibok ta sace ’yan mata
Mai magana da yawun Gamayyar Kungiyoyin Shiroro, Salis Mohammed Sabo, ya ce harin jirgin sojin ya faru ne ranar Laraba da safe a lokacin da yaran suke tsaka da diban ruwa a wata rijiyar burtsatse ta zamani a kauyen na Kurebe.
Ya bayyana cewa wani dattijo a kauyen ya rasa ’yar cikinsa da kuma jikokinsa biyu a harin jirgin.
Aminiya ta gano cewa jirgin yakin yana aiki ne tare da rundunar tsaron hadin gwiwa mai yaki da ’yan bindiga inda yake tarwatsa maboyarsu.
Jirgin yana tsaka da aikin ne ya yi kuskuren bude wa mazauna kauyen wuta, ya ragargaza gidaje da dama tare da kashe yaran.
Amma Sabo ya ce sanin kowa ne cewa kauyen ba maboyar ’yan ta’adda ba ne.
A cewarsa, “Maboyar ’yan bindiga sanannun wurare ne kuma ’yan bindigar yankin kauyen sun kasu gida biyu, kowane gungu da maboyarsa.
“Daya maboyar na hadewa da kauyen ne daga Unguwan Zomo, sai na biyun da ya taso daga yankin Kwantan Yashi.”
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin mai magana da yawun Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet, amma abin ya faskara.
Mun kira wayarsa amma layin ba ya shiga, mun tura mishi rubutaccen sako, amma babu amsa, har muka kammala hada wannan rahoto.
Kawo yanzu dai Gwamnatin Jihar Neja ba ta ce komai ba game da lamarin.