Wata tanka ɗauke da man fetur ta kama da wuta yayin da ta ke sauke mai a gidan mai na A.A. Rano da ke Kontagora, a Jihar Neja.
Lamarin ya faru ne da da misalin ƙarfe 7 na daren ranar Lahadi kusa da Asibitin Gaba.
- Gwamnonin Arewa sun yi wa Radda ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa
- ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 10, sun jikkata 14 a Zamfara
Shaidu sun ce gobarar ta fara ne yayin da ake sauke man fetur, lamarin da ya jefa jama’a cikin fargaba kasancewar sauran tankunan mai maƙare suke da fetur.
Jami’an kashe gobara sun garzaya wajen don shawo kan lamarin, amma har yanzu wutar na ci gaba da yaɗuwa.
“Babu wanda aka ruwaito ya rasa ransa, amma mutane sun tsere domin tsira da rayukansu,” in ji wani mutum, mai suna Abba Mohammed.
Ƙoƙarin jin ta bakin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, ya ci tura zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.