Aƙalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu a ranar Talata sakamakon fashewar wata tankar mai da ta tashi a Jihar Neja, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da lalata filayen noma a cikin unguwanni.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Ƙaramin Rami da ke ƙaramar hukumar Mashegu da misalin ƙarfe 6:30 na yamma.
- An yi garkuwa da ɗan uwan Bishop Kukah da wasu 6 a Kaduna
- Najeriya ta kama hanyar gyaruwa – Remi Tinubu
Rahotanni sun bayyana cewa haɗarin ya afku ne lokacin da wata motar ɗaukar kaya ta yi yunƙurin kaucewa wasu munanan hanyoyi.
Waɗanda fashewar ɗin ta rutsa da su sun haɗa da: Rafiatu Sahabi da Ramlat Shehu da Rashida Abdullahi da Raliya Abdulrahman da Zainab Ahmed, Zuwaira Idrisu da kuma Maryam A. Nura.
Wata mata mai suna Maimuna Isah ta samu raunuka kuma tana karɓar magani a cibiyar kula da lafiya matakin farko na Saho Rami.
Motar tankar dai ta kife ne ta zubar da man cikinta a kan titi, inda man ya kwarara zuwa wani rafi da ke kusa inda manoman rani ke aikin noman shinkafa.
An bayyana cewa man da ya zube ya ci karo da wani famfunan ruwa da manoman ke amfani da su, lamarin da ya sa gobarar da ta koma kan tankar da ta kai ga fashewa.
Gobarar ta mamaye filayen noma ta kuma gurɓata rafin, inda ta ƙona manoma da dama da kuma ƙone gonakin shinkafa da kayan lambu.