✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jirgin saman Ukraine da ke dauke da makamai ya yi hatsari a Girka

Dukkan mutum takwas din da ke cikin jirgin sun mutu

Wani jirgin dakon kaya da ke dauke da makaman yaki na kasar Ukraine ya yi hatsari a kasar Girka tare da kashe dukkan mutum takwas din da ke cikinsa.

A cewar Ministan Tsaron kasar Sabiya, Nebojsa Stefanovic, jirgin ya taso ne daga Sabiya zuwa Bangladash kafin ya hadun da iftila’in a kasar Girka ranar Asabar.

Shaidun gani da ido sun ce sun ga sassan jirgin na ci da wuta bayan sun jiyo karar fashe-fashe a yankin.

Wani bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta ya nuna jirgin na ci da wuta lokacin da ya fado kasa a kauyen Paleochori da ke kusa da birnin Kavala na Girkan.

“Sai dai abin takaici, bayanan da muka tattara sun nuna cewa dukkan mutanen da ke cikin jirgin su takwas sun riga mu gidan gaskiya,” inji Ministan Tsaron na Girka yayin wani taron manema labarai da safiyar Lahadi.

Jirgin dai mai suna Antonov An-12 ya taso ne daga filin jirgin saman Nis da ke Kudancin Sabiya da misalin 8:40 na daren Asabar, yana dauke da kusan tan 11 na nakiyoyi da sauran kayan yaki daga kamfanin kasar ta Sabiya, inda ya nufi Ma’aikatar Tsaron Bangladesh, inji Ministan.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Ukraine ta ce dukkan mutane takwas din da suka mutu a hatsarin ’yan kasarta ne.

“Binciken farko-farko da muka gudanar na nuni da cewa natsalar da daya daga cikin injinan jirgin ya samu ce musabbabin hatsarin,” inji Kakakin Ma’aikatar, Oleg Nikolenko, kamar yadda ya wallafa a shafin Facebook.

Tuni dai aka garzaya da wasu ma’aikatan kashe gobara asibiti da sanyin safiyar Lahadi saboda da kyar suke iya yin numfashi sakamakon hayaki mai gubar da suka shaka a wajen.

%d bloggers like this: