Rahotannin da ke fitowa daga garin Bagudo a Jihar Kebbi ya ce jirgin ruwan ’yan kasuwa daga Jamhuriyar Nijar ya nutse a cikin kogin Kwara a garin Lolo, inda kimanin mutum 53 daga cikin mutum 100 da ke cikin jirgin suka nuste inda ake tunanin sun rasu a cikin ruwan.
Tuni gwamnatin Nijar ta tura masana tukin jirgin ruwa 500 domin binciko mutanen da suka bace a cikin ruwan.
Aminiya, ta samu labarin cewa ’yan kasuwar 100 suna hanyarsu ta zuwa kasuwar da ke iyakar Jihar Kebbi da Nijar kafin jirgin ya nutse da su a Kogin Kwara da ke Jihar Kebbi.
Shugaban karamar Hukumar Bagudo, Alhaji Muhammad Zagga ya shaida wa manema labarai ta waya cewa mutum 100 da ke cikin jirgin ’yan kasuwa ne daga garin Gaya a Jamhuriyar Nijar. Ya ce, “Za su je kasuwar Lolo, kafin jirginsu ya nutse a cikin kogin.”
Ya ce an kubutar da mutum 47 daga cikinsu, yayin da sauran suka bace a cikin ruwan.
Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kebbi (SEMA), Alhaji Abbas Rabi’u Kamba ya tabbatar da nutsewar jirgin a kogin dauke da ’yan kasuwa 100 daga Jamhuriyar Nijar a hanyarsu ta zuwa kasuwar Lolo.