✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin Flynas zai kwaso rukunin farko na Alhazan Nijeriya

Za a soma jigilar kwaso alhazan Jihar Kebbi a wannan Asabar ɗin.

Jirgin Saman Saudiyya na Flynas, zai soma jigilar dawo da kashin farko na Alhazan Nijeriya a wannan Asabar ɗin.

Manajan Daraktan na Kamfanin Tafiye-Tafiye na First Planet Travels and General Sales Agent (GSA) na Flynas, Alhaji Umar Kaila, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Makkah, a kasar Saudiyya.

Ya ce, za a fara jigilar dawo da mahajjata daga jihar Kebbi ne daga filin jirgin sama na Sarki AbdulAziz da ke Jeddah zuwa filin jirgin saman Sa Ahmadu Bello (SABIA) da ke Birnin Kebbi a Jihar Kebbi.

A ranar 16 ga watan Mayu ne kamfanin Flynas ya fara jigilar maniyyata aikin hajji daga Birnin Kebbi, inda ya kwashi maniyyata 19,908 zuwa Madina a cikin jirage 48.

Kaila ya ce, “Muna farin cikin sanar da cewa Flynas ya shirya tsaf don fara aikin jigilar alhazan Najeriya daga Saudiyya zuwa Najeriya daga ranar Asabar 22 ga watan Yuni, 2024 tare da alhazan jihar Kebbi.

“Kamar yadda muka yi jigilar alhazai daga Najeriya zuwa Saudiyya ba tare da wani ɓata lokaci ba, mun tanadi tsare-tsaren dawo da alhazanmu Najeriya cikin tsari mai inganci.”