Wani jirgin saman Amurka dauke da fasinjoji ya koma Jihar Miami inda ya fito, domin ya sauke wata fasinjar da ta yi taurin kan kin sanya takunkumi.
Jim kadan da tashin jirgin, kirar AAL38 wanda ke dauke da fasinjoji 129, ’yan sanda da ke tsaye suna jira suka jagoranci sauke matar, mai kimanin shekara 40 a duniya.
- Mahara sun yi awon gaba da Kwamishina a Bayelsa
- ‘Da shinkafar bera ta N100 na yi amfani wajen kisan Hanifa’
Yanzu dai an saka sunan matar a jerin wadanda aka haramta wa yin tafiye-tafiye ta jiragen sama a Amurka, har zuwa lokacin da za a kammala bincike a kanta.
Jirgin dai ya yi saukar gaggawar ne ranar Laraba kasa da sa’a daya bayan ya tashi, kamar yadda bayanan manhajar bibiyar sauka da tashin jirage ta FlightAware ta nuna.
“Jirgin kasar Amurka wanda ta taso daga Jihar Miami zai tafi Landan ya dawo saboda wata fasinja da ta ki sanya takunkumi, kamar yadda dokar kasa ta tanada,” kamar yadda kamfanin jirgin ya sanar.
Daga bisani dai an sake samo wa fasinjojin wani jirgin da ya kai su Landan din ranar Alhamis.
Wani fasinja da ke cikin jirgin ya shaida wa kafar yada labarai ta CBS WFOR-TV cewa dukkansu sun kadu matuka da lamarin.
Kamfanonin jiragen sama a Amurka dai sun ba da rahoton cewa akalla sau 6,000 fasinjoji suna kin bin matakan kariya a bara, yayin da a bana kuma har an riga an sami mutum 151.
Akasarinsu dai mutanen da suka ki sanya takunkumi ne.