✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin Amurka ɗauke da mutum 10 ya ɓace

Jami'an tsaron gaɓar tekun Amurka sun aike da jirgin sama samfurin C-130 domin taimakawa ma'aikatan ƙasa wajen gano jirgin da ya ɓata.

Ma’aikata a Jihar Alaska da ke Amurka sun bazama neman wani ƙaramin jirgin sama na kasuwanci a ranar Juma’a da ya ɓace ɗauke da mutum 10.

Kamar yadda hukumomin yankin suka ce, a wani sabon afkuwar da ya afku ta jirgin Amurka.

Rundunar ’yan sandan Jihar Alaska ta sanar da cewa, jirgin samfurin Cessna Caraɓan mai fasinjoji tara da matuƙin jirgi ɗaya ne, an samu rahoton ne ranar Alhamis.

Jirgin da ya tashi daga Unalakleet zuwa Nome da ƙarfe 4:00 na yamma agogon Alaska (0100 GMT) da ya ɓace.

Biranen biyu suna da nisan mil 146 (kilomita 235) da juna a fadin Norton Sound, a gabar yammacin jihar.

Cikin wata sanarwa da hukumomin jihar suka fitar, sun ce ma’aikatan ceto na cigaba da ƙoƙarin gano wurin da yake.

Ma’aikatar kashe gobara ta Nome ta ce, a cikin wani saƙon da ta wallafa a shafin Facebook na cewa, “matukin jirgin ya shaida wa hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Anchorage cewa “ya yi niyyar shigar da wani tsari ne yayin da yake jiran umarni kafin ya ɓace.

Ma’aikatar ta ƙara da cewa, jami’an tsaron gaɓar tekun Amurka sun aike da jirgin sama samfurin C-130 domin taimakawa ma’aikatan ƙasa wajen gano jirgin da ya ɓata.