Wani jirgin sama dauke da Babban Hafsan Tsaron Indiya, Janar Bipin Rawat, ya yi hatsari a Jihar Tamil Nadu da ke Kudancin kasar, inda ya kashe mutum hudu.
Kafafen yada labarai a kasar sun rawaito hatsarin na ranar Laraba, inda suka ce mutum hudu sun mutu, uku kuma sun ji rauni kuma tuni aka garzaya da su asibiti.
- Yawan ’yan Najeriya da ke cikin kangin talauci zai kai miliyan 109 a 2022 – Gwamnati
- Dalilan da mata ba sa kaunar junansu
Sai dai har yanzu babu sanarwa a kan haka a hukumance.
Rundunar Sojin Saman kasar dai a ranar Laraba ta wallafa a shafinta na Twitter cewa, “Jirgin helikwafta samfurin IAF Mi-17V5, dauke da Babban Hafsan Tsaro, Janar Bipin Rawat, ya yi hatsari yau a kusa da Coonoor da ke Jihar Tamil Nadu.”
Sai dai sanarwar bat a fayyace ko Babban Hafsan mai kimanin shekara 63 ya ji rauni a hatsarin ba.
Ana dai jiran Ministan Tsaron Kasar Rajnath, ya fitar da sanarwa anjima a gaban Majalisar Kasar ranar Laraba.
Har zuwa yanzu dai ba a san ainhin adadin mutanen da ke kan jirgin ba, amma wasu kafafen yada labaran kasar sun nuna wata takarda da ke dauke da sunan mutum tara, ciki har da matar Babban Hafsan da kuma wasu manyan jami’an sojin kasar.
Rahotanni dai sun ce jirgin na kan hanyarsa ne daga sansanin Sojin Saman kasar zuwa Makarantar Horar da Manyan Dakarun sojoji lokacin da ya yi hatsarin a Jihar ta Tamil Nadu.
Wasu faya-fayan bidiyo dai sun nuna wasu sassan jirgin na ci da wuta, yayin da mazaunana yankin ke kokarin kashe wutar da ke ci a cikinsa.