✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jiragen yaki sun yi wa ’yan bindiga luguden wuta

Jiragen sun yi luguden wuta na awanni kan maboyan ’yan bidiga da masu garkuwa.

Jiragen sojin saman Najeriya sun yi luguden bama-bamai a kan maboyan ’yan bidiga da masu garkuwa da mutane a Jihar Nasarawa.

Tun da misalin karfe 9 na safiyar ranar Lahadi ne jiragen yakin suka fara shawagi a yankin, kafin su fara ruwan wuta na tsawon awa uku tun daga misalin karfe 10 na safen.

Luguden wutan jiragen yakin na tsawon awa uku a yankin Giza da Karamar Hukumar Keana ta Jihar ya sanya zullumi a zukatan mazauna.

Rugugin harbe-haben ya sa mazauna yankunan da ke kan iyakar Jihar ta Nasarawa da makwabciyarta, Binuwai kaura daga gidajensu domin tsira da rayukansu.

Binciken wakilinmu ya gano yadda jiragen suka yi fata-fata da wasu shanu da ake kyautata zaton wadanda ’yan bindigar suka sace ne.