Jiragen Rundunar Sojin Sata ta Najeriya sun kashe ’yan bindiga 17 tare da tarwatsa sansanoninsu a Dajin Dunya na Jihar Katsina.
Jami’in Yada Labaran Rundunar Tsaro, Manjo Jana John Enenche ya ce jiragen rundunar “Operation Hadarin Daji” sun yi wa ’yan bindigar ruwan wuta ne a ranar Alhamis bayan samun bayanan sirri.
- Manoma na biyan ’yan bindiga haraji kafin su yi girbi a Zamfara
- Kotu ta sa ’yan sanda su biya matashi diyyar Naira miliyan uku
- Mun ceto mutum 100 daga kangin bauta —Masari
Enenche ya ce rundunar ta samu bayanai cewa ’yan bindiga masu alaka da kungiyar Ansaru sun yi sansani a dajin inda suke tara shanun sata.
Nan take a cewarsas aka tura jiragen yaki suka suka kuma yi nasarar halaka bata-garin da kuma tarwatsa maboyar tasu ma’ajiyarsu.
Ya ce daga baya bincike ya gano cewa an kashe ’yan bindiga sama da 17 baya ga wasu da dama da suka samu raunuka.
“Hedikwatar Tsaro na yaba wa sojoji da sauran hukumomin tsaro a yankin Arewa maso Yamma saboda kwarewarsu, tana kuma rokon su da su kara azma domin kawar da ’yan bindiga”, inji shi.