✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jiragen yaki sun hallaka ‘yan ta’adda 7 da ake nema ruwa a jallo a Kaduna

An yi nasarar kashe 'yan ta'addar da suka addabi Jihohin Zamfara da Kaduna.

Jiragen yakin sojin Najeriya sun hallaka wasu shugabannin ‘yan ta’addan Zamfara guda bakwai da ake nema ruwa a jallo.

An ruwaito cewar an kawar da ‘yan ta’addan da suka yi kaurin suna a Jihar Kaduna sakamakon harin da jiragen yakin sojojin saman Najeriya biyu suka kai musu.

Rahotanni sun ce wadanda aka kashe sun hada da Jibrin Gurgu da Isah Jauro da Tambuwal daga Jihar Zamfara.

Sauran da aka kashe sun hada da Noti, Bala da Yunusa da Burti wanda ya kasance sanannen abokin wani dan ta’adda da ake nema ruwa a jallo, Haladu Buharin Yadi.

Wani jami’in leken asirin tsaro ya shaida wa jaridar PRNigeria cewa, farmakin ya yi sanadin kashe ’yan ta’addan da ake nema ruwa a jallo.

Ya ce dakarun rundunar tsaro ta Operation Whirl Punch ne suka kai farmakin a maboyar ’yan ta’addan da aka gano a unguwar Alhaji Ganai, Sabon wurin Buhari da Dogo Maikaji, duk a cikin Karamar Hukumar Giwa.

Ya ce: “Ida za ku iya tunawa, hare-haren sun samu nasara ne daga sahihan bayanan sirri daga majiyoyi masu inganci kan ayyukan ta’addanci a yankin baki daya.

“Saboda haka, an ba da izinin kai hare-haren ne a ranar daya ga Disamba 2022. An kai hare-hare ta sama a kan ‘yan ta’adda da kuma yankunan Tsofa da Riyawa a Kananan Hukumomin Igabi da Birnin Gwari a Jihar Kaduna.”

A cewar jami’in, bayanan da aka samu sun kuma nuna cewa ‘yan ta’addan sun gamu da ajalinsu ne sakamakon ruwan wuta da aka yi musu.

Ya ce: “Tun daga lokacin da kwamishinan Tsaron da Al’amuran Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar da wannan harin ta sama, a wata sanarwa da ya fitar a ranar biyu ga watan Disamban 2022, ya ce harin da sojojin sama suka kai sun gano tare da tarwatsa sansanin ’yan ta’adda takwas tare da kubutar da mutum 10 da aka yi garkuwa da su.”

Edward Gabkwet, mai magana da yawun Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Iya Kwamando Edward Gabkwet, ya tabbatar da harin da suka kai.

Ya gode wa ’yan Najeriya kan goyon bayan da suke bai wa rundunar da sauran jami’an tsaro, wadanda ke taimaka wa nasarorin da sojojin Najeriya suke samu a kan ’yan ta’adda.