A karo na hudu a mako guda, gwamnatin Habasha ta sake kai wani hari ta sama a Mekele, babban birnin yankin Tigray.
Rundunar sojojin kasar Habashan sun ce sun kai harin ne kan cibiyoyin da kungiyar ’yan tawayen Tigrayan suke amfani da su wajen horas da ’yan ta’adda.
An kai harin ne bayan Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin yiyuwar samun karancin man fetur a yankin na Tigray.
Ta kara da cewa yanzu haka manyan motoci 14 makare da man fetur sun makale a kan iyakar yankin, lamarin da ya tilasta kungiyoyin bada agaji dakatar da ayyukansu a yankin duk da cewa mutane da yawa a yankin na fama da yunwa kuma sun dogara ne kadai da taimakon da ake ba su.