Mutane da dama ake fargabar sun mutu bayan wasu jiragen yakin Amurka sun yi hatsari lokacin da suke tsaka da sinitiri a Jihar Kentucky ta Amurkan.
Hukumomin sojin kasar sun ce hatsarin ya auku ne wajen misalin karfe 11:00 na dareb Laraba lokacin da suke ba da horo a yankin Trigg, yamma da sansanin sojoji na Fort Campbell.
- Mamallakin Manchester City ya zama Mataimakin Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa
- ’Yan bindiga sun sake kashe mutum 3, sun sace wasu 16 a kauyukan Kaduna
A cewar kafar yada labarai ta NBC, ’yan sanda a Jihar ta Kentucky sun tabbatar da cewar jami’ansu da wasu sojoji masu bincike da ma wasu ma’aikatan ceto da dama sun yi wa wajen da hatsarin ya faru kawanya.
Hukumomin sun ce, “Muna sanar da cewa jiragen yakinmu daga sansani na 101 sun yi hatsari a daren jiya [Laraba], inda mutane da dama suka mutu,” kamar yadda sashen na sansanin 101 din ya sanar a wani sakon da ya wallafa a shafin Twitter da sanyin safiyar Alhamis.
“Yanzu haka hankula sun fara komawa kan sojoji da iyalansu da hatsarin ya ritsa da su.”
Amma a cikin wani sako da shi ma ya wallafa a shafinsa na Twitter, Gwamnan jihar ta Kentucky, Andy Beshear, ya yi kira da a yi wa wadanda abin ya shafa addu’a, inda ya ce ma’aikata na aiki tukuru wajen aikin ceto.