✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jiragen soji sun kashe ’yan ta’adda 28 a Neja

’Yan bindiga kimanin 100 ne suka yi musayar wuta da su a yankin Bassa

’Yan bindiga akalla 28 ne jiragen sojin saman Najeriya suka hallaka a yankin Bassa,  Ƙaramar Hukumar Shiroro a Jihar Neja.

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta ce jiragen sun ragargaji ’yan ta’addan ne da hadin gwiwar sojojin ƙasa.

Mataimakin Darakta Yaɗa Labarai na Rundunar, Kyaftin Kabiru Ali, ya ce a yayin aikin sharar ’yan fashin daji ne sojojin suka yi arba da gungun wasu ’yan ta’adda kimanin 100.

Kyaftin Ali ya ce, “da samun rahoto ne jiragen suka je suka ragargaji ’yan ta’addan, inda aka gano gawarwakin 28 daga cikinsu.

“A halin yanzu ana ci gaba da kwaso makamansu da ababen hawansu, ana neman sauran ’yan ta’addan,” bayan harin na ranar Laraba, in ji sanarwar.

Jami’in ya bayar da tabbacin cewa rundunar za ta ci gaba aikin tabbatar da tsaron jama’ar da murƙushe duk wata barazanar tsaro da ragowar ’yan ta’adda da ke hana jama’a sakat.