✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirage 30 za su debi ’yan Maroko zuwa kallon wasan kasar da Faransa

Jiragen za su tashi daga Maroko ne zuwa Doha a Qatar

Kamfanin Jiragen Sama na kasar Maroko ya ware jirage 30 da za su yi jigilar magoya bayan tawagar kasar zuwa Qatar domin kallon wasan dab da na karshe tsakanin kasar da Faransa.

Kamfanin na Royal Air Maroc ya sanar a ranar Litinin cewa zai kwashi mutanen ne daga Kasablanka, babban birnin Maroko zuwa Doha, babban birnin Qatar a ranakun Talata da Laraba.

Maroko dai ta kai matakin ne bayan ta doke kasar Portugal da ci daya mai ban haushi a ranar Asabar, nasarar da ta sa ta kafa tarihin zama kasar Larabawa da kuma ta Afirka ta farko da ta kai matakin na dab da wasan karshe a tarihin gasar.

Kamfanin na Maroko dai ya ce, “Irin bajintar da tawagar kasarmu take nuna a Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa ta Duniya ta 2022 ba za a taba mancewa da ita ba tarihin kasar.

“Saboda haka, domin mu ba ’yan kasarmu da dama da ke goyon bayan tawagar zarafin zuwa su je su taya su fatan alheri a wasansu da Faransa…Kamfanin Royal Air Maroc ya jera jirage 30 daga Kasablanka zuwa Doha,” inji sanarwar.

Kamfanin ya ce zai rangwanta farashin tikitin jirgin ne a kan kudin kasar Dirham 5,000, kwatankwacin Dalar Amurka 472.

An shirya jigilar ce tare da hadin gwiwar Hukumar Wasannan kasar da kuma Ma’aikatar Wasanninta.

Za a buga wasan dab da na karshen ne tsakanin Maroko da Faransa ranar Laraba a filin wasa na Al-Bayt da ke unguwar Al-Khor da ke Arewacin birnin Doha na Qatar.