An ayyana jihohin Ondo, Bayelsa da Legas a matsayin inda aka fi tsananin fama da tsadar kayayyaki a Najeriya a cikin watan Maris na wannan shekara.
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, hakan ya bayyana ne a cikin wasu alkalumma da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar a kan tsadar kayayyaki a fadin kasar a ranar Asabar.
- Babu lallai a ga jinjirin watan Shawwal a ranar Alhamis —Masana
- Yadda jam’iyyu suka kacaccala kujerun sanatoci a Zaben 2023
A cewar NBS, hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya a watan Maris na shekarar 2023 ya karu zuwa kashi 22.04 cikin 100 idan aka kwatanta da na watan Fabrairun 2023 wanda ya kai kashi 21.91 cikin 100.
Wannan ya nuna karuwar maki 0.13 cikin 100 idan aka kwatanta da rahoto kan tsadar kaya na watan Fabrairun 2023.
A matakin wani bangare na kasa, “Hauhawar farashin kayayyaki a kowace shekara ya kasance mafi girma a Ondo (kashi 25.38), Bayelsa (kashi 24.80), Legas (kashi 24.66).”
A gefe guda kuma, jihohin Borno, Kuros Riba, da Sakkwato da Benuwe, sun sami hauhawar farashin kayayyaki mafi kankanta a shekara, inda aka samu hauhawar kashi 19.18, kashi 19.24 da kuma kashi 20.01 cikin dari a jihohin.
A lissafin daga wata zuwa wata, Maris din 2023 an sami karuwar tsadar kayayyaki mafi girma a Jihar Bayelsa (kashi 2.58).
Jihar Nasarawa (kashi 2.54), Jihar Legas (kashi 2.41), yayin da Jihar Anambra (1.03%), Ebonyi (kashi 1.14) kana Jihar Zamfara tana da makin (kashi 1.27 cikin dari) adadin mafi karanci a hauhawar farashin kayayyaki a duk wata.
Dangane da hauhawar farashin kayan abinci na matakin shekara, Jihar Kwara ta kasance da maki mafi girma da kashi 28.84 cikin 100.
Jihar Ondo ta biyo baya da kashi 28.22 cikin 100 sannan Jihar Legas ce a matsayi na uku da kashi 27.92.
Jihohin da aka fi samun raguwar hauhawar farashin kayan abinci sun hada da Jihar Sakkwato, mai kashi 18.99, Jihar Zamfara mai kashi 20.75 sai kuma Jihar Filato mai kashi 21.83.