✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihohi 34 za a iya samun rikici a lokacin zabe —Gidauniyar CLEEN

Baya ga matsalar tsaro a jihohi 21, wasu 13 kuma na fuskantar barazanar barkewarta

Gidauniyar CLEEN ta ce jihohi 34 a Najeriya na ciki ko suna fuskantar barazanar tsaro da tashin hankali a lokacin babban zabe da ke take.

Rahoton kungiyar ya ce jihohin Kano, Jigawa da Abuja ne kadai ke da cikakken amincin da za a iya gudanar da zaben da za a fara nan da mako uku masu zuwa.

Babban Darakan CLEEN, Gad Peter, ya ce, “Yawan hare-haren da ake kai wa cibiyoyin tsaro da ofisoshin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a ’yan watannin nan abin damuwa ne da kuma Allah wai; kuma wata dabara ce ta bata-gari masu son wargaza Najeriya.”

Binciken ya nuna cewa baya ga matsalar tsaro a jihohi 21, wasu 13 kuma na fuskantar barazanar barkewarta, ciki har da jihar Sakkwato, Kebbi, Neja, Binuwai, Gombe, Bauchi, Filato, Nasarawa, Taraba, Edo, Delta, Akwa Ibom da kuma Abiya.

Rahoton ya ce abubuwan da ke iya haifar da rikici sun hada da yaudarar talakawa, jahilci, rashin sanin dokar zabe, matsalar sabuwar na’urar tantance masu zabe ta BVAS, bangar siyasa da kuma rashin kyan hanyar isa wasu yankuna domin gudanar da zabe.

“Gidauniyar CLEEN ta damu da irin miyagun kalaman raba kan jama’a da na nuna tsana da kuma hare-haren da ake kai wa ’yan sanda da cibiyoyin INEC, wadanda idan ba a magance su ba, za su kawo tarnaki ga zaben da kuma zaman lafiya da hadin kan kasar nan,” in ji shugaban kungiyar.

Abin da ya kamata

Binciken da kungiyar ta yi domin gano kan yanayin tsaro da kuma alakarta da zaben da ke tafe a fadin Najeriya ya ba da shawarwaki kan yadda za a shawo kan masalolin domin gudanar da zabe mai inganci da kuma samun karbuwa cikin nasara.

Ya ce wajibi ne hukumomin tsaro su dauki matakan da suka dace wajen da dakile duk wata barazana ko hari domin ba wa ’yan kasa kwarin gwiwar fitowa su yi zabe.

“Sanannan abu ne cewa a wannan karon ne aka samu masu rajisar zabe fiye da kowane lokaci a tarihin Najeria, amma za a iya rasa duk nasarar idan aka bar bata-gari suna kai hari ko barazana ga jama’a ko rikici ko kalaman tsana, wanda hakan zai hana muane fitowa su yi zabe.

Ya ce binciken ya gano, ’yan Najeriya musamman matasa na da kwarin gwiwa game da zaben, ganin irin yadda suka fito da yawa suka yi rajistar zabe bayan dokar zabe ta amince da amfani da nau’arar BVAS wajen tantace masu zabe da kuma tura sakamon zabe ta intanet daga rumfar zabe.

Rahoton gidauniyar ya ce hakan na nuna yadda matasan ke da kwarin gwiwa kan fasahar zamani, da kuma yadda suka yi amanna cewa fasahar za ta toshe kofar yin magudi.