✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihar Shugaban PDP ta juya wa Atiku baya

Dattawan Binuwai da Gwamna Ortom sun janye goyon bayansu ga Atiku a zaben 2023, duk da cewa daga Jihar Binuwai Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa,…

Gwamnan Binuwai, Samuel Ortom da dattawan jihar sun yi hannun riga da dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Ortom wanda dan PDP ne tare da dattawan sun janye goyon bayansu ga Atiku a zaben 2023, duk kuwa da cewa daga Jihar Binuwai Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Iyorchia Ayu, ya fito.

A cewarsu, sun yi raba gari da Atiku ne, saboda ba ya nufin Jihar Binuwai da jama’arta da alheri.

Kalaman Ortom din na zuwa ne bayan Kungiyar Dattawan Binuwai ta Minda sun bar ranta kansu daga Atiku, bisa zargin sa da yin kalaman tsana ga mutanen jihar da kuma yi musu kudin horo.

Ortom ya yi wannan jawabi ne a matsayin raddi ga kalaman Atiku game da harin kwanan da ake zargin makiyaya sun kai wa manoma a Binuwai.

Ortom wanda na hannun daman Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, wanda tuni ya raba gari da Atiku, ya zargi dan takarar da goyon bayan kungiyar makiyaya taMiyetti Allah.

Ya bayyana a cocin Chapel of Grace da ke Gidan Gwamnatin Jihar Binuwai a Makurdi, ranar Talata cewa, “Ba daidai ba ne dan takarar shugaban kasa ya yi irin wannan furucin.

“Babban kuskure ne, kuma wannan na iya alamta cewa bai dauke ni a matsayina na Gwamnan Jihar Binuwai ba.”

Ortom ya kuma zargi Atiku da mayar da shi saniya ware wajen zaben mambobin kwamitinsa na yakin neman zaben 2023.

Ya ce, “Ba na cikin kwamitin yakin neman zabensa, kuma ba da sanina aka mutanen da suka nada ba.

“Saboda haka babu ruwan, zan koma gefe, amma zan jira in gani, idan lokacin zabe ya zo, za mu yi shi yadda ya zo.”

‘Ortom bai kyauta ba’

Amma a martaninsa ga bayanin na Ortom, mamba a Kwamitin Yakin Neman Zaben Atiku, Dele Momodu, ya ce gwamnan bai kyauta ba.

Dele More ya ce, “Kuskure ne ya kira shi (Atiku) wakilin Miyetti-Allah, wannan bai dace ba.

“Ra’ayinsa ne fadin duk abin da ya ga dama a game da Atiku Abubakar, amma idan ya ce masa wakilin  Miyetti Allah, wannan ne ba zan taba yadda ba.

“Idan ba za ka goyi bayansa ba a ba laifi ba ne, . . . ba sai ka goga masa kashin kaji ba.

“Kuskure ne ka yi irin wannan miyagun kalama ga mutumin da ya bauta wa kasarsa…amma saboda ka samu sabanin siyasa da shi ka rika yi masa irin wannan mummunan kaje.

“Amma, gaba ta fi baya yawa,” inji Dele Momodu.

Ya ce, “Ko Wike, wanda ya kamata a ce ya fi sauransu fusata saboda ya nemi takara a jam’iyyarmu ba zai yi irin wannan lafazin ba.”

Bangaren Wike

Ortom na daga cikin gwamnonin PDP magoya bayan Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike m wanda Atiku Abubakar ya kayar a zaben dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP.

Sauran takwarorinsa su ne Gwmana Seyi Makinde na Jihar Oyo da Okezie Ikpeazu na Jihar Abia.

Bangaren na Wike sun dade suna neman a kori Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Iyorchia Ayu, wanda ya fito daga Binuwai, a maye gurbinsa da dan Yankin Kudu.

Sun yi zargin cewa Ayu, wanda dan Arewa ne, ya yi alkawarin sauka daga mukaminsa idan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ya fito daga yankin.

Sai dai kuma tuni Ayu ya bayyana cewa ba zai sauka daga mukaminsa ba, sai akalla bayan zaben shugaban kasa da za a gudanar a watan Fabrairu, 2023.