Gwamnatin Jihar Neja ta sallami jami’anta guda 80 a ma’aikatu daban-daban bisa kama su da al’mudahanar miliyoyin kudi.
Shugabar Ma’aikata Jihar, Hajiya Salamatu Tani Abubakar ce ta bayyana wa ‘yan jarida haka bayan fitowa daga taron manyan makaraban gwamnatin jihar a ranar Alhamis.
- Sai masoyan Buhari sun biya zan saki sabuwar waka —Rarara
- Buhari ya yi wa Bulama mai zane barkwanci wasika
Tani ta ce, ma’aikatan da aka sallama suna matakan ayyuka ne daban-daban kuma ana ci gaba da bincike don zakulo sauran bata-garin.
Shugabar Mai’katan ta ce, ma’ikatan sun amsa laifukansu a gaban kwamitin binciken albashi da gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello ya kafa, kuma a yanzu haka Hukumar Ma’aikatan Jihar na kokarin rubuta musu takardun sallama.
“Ma’aikatun da abun ya shafa sun hada da: Hukumar Kula Asibitocin Jihar, mutum 45; Hukumar Shari’a, mutum 22; Hukumar Lafiya a Matakin farko, mutum 3; Ma’aikatar Lafiya, mutum 7; Ma’aikatar Ilimi mutum 1; Makarantar Ungozoma ta Minna da kuma Tunga Magajiya mutum 1 da 2 kowannensu”.
Tani ta kuma ce kwamitin na ci gaba da bincike kuma a yanzu ba zai iya bayyana yawan ma’aikata ko kudi da za su iya ganowa ba amma duk wanda aka kama da laifi zai fuskanci hukunci.