Gwamnatin Kebbi ta sauya kirar wasu motocinta ta mayar da su masu sukmlke a kokarinta na yakar ’yan bindiga a Jihar.
Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Samaila Yombe, ya ce jifa-jifai 10 kirar Landcruiser ne aka mayar masu sulke domin samar wa sojoji kayan aikin da suka dace wajen yakar ’yan bindiga.
- ’Yan bindiga sun karkashe juna a musayar wuta
- ‘Ba zan sauka daga mulki ba har sai na kawo karshen matsalar tsaro’
“Karafan da muka sauya wa jikin motocin za su kare direba da sauran sojojin da ke ciki daga hari, ga shi kuma an yi wa motocin wurin daura bindiga,” inji Yombe, wanda tsohon Kanar din soja ne.
Da yake kaddamar da motocin a Birnin Kebbi, babban birnin jihar, Yombe, wanda ya jagoranci sauya kirar motocin ya ce an yi su ne da karko ta yadda sojoji za su iya amfani da su su shiga kowane irin wuri a jihar.
Mataimakin Gwamnan wanda shi ne da kansa ya sauya zanen taswirar motocin zuwa na yaki y jaddada muhimmancin samar da nagartattun ababe sufuri a aikin soji wajen saukake jigilar kayan yaki da dakarun.