Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya sa hannu kan dokar kafa hukumar kula da safarar magunguna da kayayyakin jinya a jihar.
Kakakin gwamnan, Isma’ila Uba Misilli ne ya bayyana haka a sanarwar da ya rabawa ƴan jaridu.
Sanarwar ta ce tun ranar 18 ga Mayu Majalisar Dokokin jihar Gombe ta amince da ƙudirin dokar.
Matashiya mai yi wa kasa hidima ta mutu a Gombe
Majalisar Gombe ta amince Gwamna ya nada mashawarta 30, ya kara wa Ciyamomi wa’adi
Haka kuma ta ce hukumar za ta kasance sahihiyar hanya ta samar da magunguna da kayayyakin jinya masu inganci da rahusa ga al’ummar jihar.
Bayan haka, sanarwar ta buƙaci haɗin kan al’amu domin samun nasarar hukumar.