✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Gombe ta amince Gwamna ya nada mashawarta 30, ya kara wa Ciyamomi wa’adi

Ciyamomin za su ci gaba da mulki har watan Disamba mai zuwa

Majalisar Dokokin Jihar Gombe ta amince wa Gwamna Muhammad Inuwa, ya nada masu ba shi shawara guda 30.

Wannan batu yana dauke ne a wata takarda da mai magana da yawun majalisar, Japheth Bekeri Idi,  ya fitar ranar Alhamis, aka raba wa manema labarai a Gombe.

Takardar ta nuna cewa  a jawabinsa ga manema labarai a zauren majalisar, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Yerima Ladan Gaule, kira ya yi  ga wadanda za su rabauta da mukaman da su ba Gwamnan shawarwarin da ya kamata da zai ba shi ikon gudanar da ayyukan raya kasa masu muhimmanci a Jihar.

A wani labarin kuma, biyo bayan karewar wa’adin Shugabanin riko na Kananan Hukumomin Jihar a ranar Litinin din da ta gabata, Majalisar ta amince wa Gwamnan ya tsaiwata wa’adinsu da watanni shida zuwa watan Disamban 2023.

Hakan ya biyo bayan rokon da Gwamnan ya yi wa majalisar ce a wata takarda da Akawunta, Barista Rukayyatu Jalo, ta karanta a gaban Majalisar.

Da yake gabatar da kudurin a gaban majalisar mamba mai wakiltar mazabar Yamaltu ta Gabas, Alhaji Adamu Saleh Pata, ya ce tsawaita musu wa’adin ya dace inda ya ce a tsarin gwamnati akwai ci gaba wato dorawa daga inda aka tsaya,

Ya kara yin kira ga Shugabanin rikon kwaryar da su gane cewa tsakanin majalisa da Shugabannin riko kwaryar akwai alaka wajen ciyar da jihar gaba da dora ta a kan turba mai kyau.