Rahotanni na nuna cewa shugaban ‘yan shi’a na Jihar Sakkwato, Malam Kasim Umar ya rasu bayan ya yi fama da jinya.
Malam Kasim ya rasu kimanin mako biyu bayan da aka harbe shi a lokacin da suke zangar-zangar ganin an saki shugabansu na kasa Sheikh Ibrahim Zakzaki a Abuja.