Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta kasar Saudiyya (GACA) ta amince wa kamfanonin jiragen sama na Najeriya su kara yawan sawun da suke yi wajen kwaso alhazan kasar zuwa gida bayan kammala aikin Hajjin bana.
A bisa haka, a kullum kamfanonin za su iya yin sawu 15 na alhazai daga Kasa Mai Tsarki zuwa Najeriya mai alhazai 95,000 da suka sauke farali a bana.
- Mun kama tirela 37 makare da shinkafa ’yar waje a Ogun – Hukumar Kwastam
- Cutar Diphtheria ta kashe yara 30 a Yobe
Bisa amincewar da GACA ta yi, daga ranar Laraba, kowanne daga cikin kamfanonin zai iya yin sawu biyar na alhazai daga Saudiyya zuwa Najeriya.
Hukumar ta ba da izinin ne sakamakon tafiyar hawainiya da aikin kwaso alhazan zuwa gida yake yi, a yayin da alhazai ke bayyana kosawarsu su dawo gida bayan sauke faralin.
A mako guda da aka fara dawo da alhazan, zuwa yanzu sawu 19 na alhazai kimanin 11,000 aka yi daga cikin ’yan Najeriya da suka je aikin Hajjin.
A baya dai hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta sanar cewa za ta kammala aikin cikin kwana 30.
Kamfanonin cikin gida da ke jigilar alhazan dai su ne Aero Contractors, AZMAN, Air Peace, Max Air da kuma Arik.
Da farko hukumar sufurin jiragen sama na Saudiyya ta ki amincewa da bukatar ta NAHCON, duk da cewa Jakadan Najeriya kasar Dauda Yahaya Lawal ya sanya baki.
A karshe sai da maganar ta kai ga shugabannin kasar, inda suka share wa Najeriya hawaye.
Alhazai kimanin 95,000 ne daga Najeriya suka yi aikin Hajji a bana, cikinsu har da mutum 5,000 ’yan jirgin yawo
Zuwa yanzu sawu akalla 26 aka yi, inda aka kwashe alhazai 11,416, wadanda Flynas ne ya yi jigilar kashi biyu bisa ukunsu.