✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun kama tirela 37 makare da shinkafa ’yar waje a Ogun – Hukumar Kwastam

An kama shinkafar ne a cikin wata shida

Hukumar Kwastam ta Najeriya a ranar Talata ta ce ta kama wasu tireloli 37 makare da shinkafa ’yar kasar waje a sassan Jihar Ogun daban-daban.

Hukumar, ta bakin ofishinta da ke Jihar ta Ogun ya ce an kama motocin ne a tsakanin watan Janairu zuwa Yunin bana.

Kazalika, ta kuma ce ta kwace man fetur kimanin lita 173,975, kwatankwacin tanka biyar, sannan ta kama masu fasakwauri bakwai.

Kwanturolan hukumar a Jihar, Bamidele Makinde ne ya bayyana hakan ranar Talata, lokacin da yake jawabi ga manema labarai kan nasarorin da hukumar ta samu a wata shida na farkon shekarar nan, a hedkwatarsu da ke Idiroko.

Ya kuma ce sun kama wasu motocin alfarma da aka yi fasakwaurinsu ta kan iyakar tsandauri ta Ohumbe a Jihar.

Bugu da kari, ya ce hukumar ta tara kudaden shigar da yawansu ya haura Naira miliyan 93 daga kudaden fito da sayar da man fetur da kuma tsofaffin ababen hawa.

Bamidele ya ce hakan kuma yana nufin kudaden sun karu da kimanin kaso 310 cikin 100 na wadanda aka tara a bara, wadanda ba su wuce miliyan 29 ba, a makamancin wannan lokacin.

Bugu da kari, ya ce sauran kayayyakin da suka kama sun hada da tayoyi 5,048 da dilar gwanjo 390 da motoci 61, ciki har da 5 na alfarma da litar mai 173,975.

Kazalika, ya ce jami’an hukumar sun sami nasarar kama miyagun kwayoyi da suka hada da buhu 107 da kuma kulli 1,595 na tabar wiwi sai katan 194 na maganin tari na Kodin sai kuma shinkafa ’yar waje buhu 22,526 mai nauyi kilogiram 50 (kwatankwacin tirela 37).