✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Babu hannun malaman jami’a a magudin zabe a Najeriya’

Ya ce malaman jami'a mutanen kirki ne, babu ruwansa

Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a Jihar Kaduna, Farfesa Kabir Bala ya musanta zargin yin amfani da malaman jami’a wajen tafka magudin zabe a Najeriya.

Ya ce malaman, mutane ne masu ilmi da hangen nesa da ba su yarda a yi amfani da su ba wajen kawo wa kasa nakasu ta kowace fuska.

Farfesa Kabir ya bayyana hakan ne bayan kammala wani taro na kasa da kasa karo na uku akan harkokin zabe, wanda Sashen Kimiyyar Siyasa da Harkokin Kasashen Waje na jami’ar ya shirya a Zariya.

Farfesan ya kuma nuna rashin jin dadin shi bisa yadda jama’a ke zagin malaman jami’ar a kan yadda suka gudanar da zabubbukan da suka gabata, ciki kuwa har da ’yan uwansu masu koyarwa.

Ya ce wake daya ba ya bata gari, kuma don an sami mutane kalilan da irin wadannan laifufukan, bai kamata a yi masu kudin goro ba.

A cewarsa, a kowane nau’i na jama’a dole a samu wasu da zasu zama bata gari, amma kuma sai a duba wadanne ne suka fi yawa daga a tsakanin baragurbi da kuma nagari.

A jawabinta a wajen taron, Shugabar Sashen Kimiyya Siyasa da Harkokin Kasashen Waje na jami’ar, Dokta Rahanatu Lawal ta ce an shirya taron ne kusan watanni biyu bayan kammala zabubbukan kasa, kuma zai bayar da damar yin waiwaye ga irin nasarori da kuma akasin haka.

Ta ce taron zai ba da mafita tare da zakulo hanyoyin bunkasa harkokin zabubbukan kasa a nan gaba.

Shi ma a nashi jawabin, bako mai jawabi, tsohon Shugaban Jami’ar Abuja, Farfesa Nuhu Yakuq, ya bai wa Hukumar Zabe ta Kasa shawarar ta koma tsarin da zai rinka ba mata cikakkiyar dama don shiga cikin zabubbuka na kasa.