✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jifar Shedan

A wajan jifar shedan ne wani Bazzazagi da karambani sai ya ce shi a sama zai yi tasa jifar. Ga shi kato ne kuma baki…

A wajan jifar shedan ne wani Bazzazagi da karambani sai ya ce shi a sama zai yi tasa jifar. Ga shi kato ne kuma baki kirin da shi, ga muni. Ya hau sama ya fara jifa ke nan sai jikkar kudinsa ta tsinke ta sullubo kasa. Gogan naku yana ganin haka, sai ya biyo abarsa suka yo kasa, yana kokarin sai ya cafki jikkarsa. Yana fadowa kasa, su kuwa alhazai sai suka ga kato a gabansu sai suka yi zaton shedan ne ya ji jifa ya bayyana a fili. Kawai sai suka ci gaba da antaya masa jifa, wasu ma har da takalmi; suna cewa: “Alugungumi, yau sai mun ga bayanka.” Shi kuwa sai ihu yake, yana cewa: “Ana insanun fi Zariya, Najeriya” (Ma’ana: Ni mutum ne dan Zariya, Najeriya). Da kyar wani Bakano ya cece shi!
Daga Shehu Mustapha Chaji, Kano