Daidai misalin karfe 8:30 na safe, Alhaji Baba ya fito daga gidansa da nufin tafiya shagonsa da ke Kantin Kwari. Ya fito hanya sosai, tuki yake alhali ransa cike da tunani iri-iri. Tunaninsa na farko shi ne, yadda zai tafiyar da matsalar da ta kunno kai tsakaninsa da matarsa. A lokacin da ya natsa cikin kai-komo da tunani, gefe daya kuma rediyon motarsa na ta fitar da sautin waka, abin da ya kara dugunzuma masa kwakwalwa. Nan take ya sanya hannu ya latsa maballin rediyon, shiru ya bayyana.
“Gaskiya bai kamata in isa shago da wannan matsalar a tare da ni, ba tare da na samo ruwan kashe ta ba.” Magana yake shi kadai kamar wanda ya tabu. Nan da nan ya tuno da abokinsa, Mamman Tela, malamin makaranta a Kwalejin Sa’adatu Rimi. Bai bata lokaci ba ya dauko waya, ya danna lambarsa. Cikin dakika kadan ya sanar da shi cewa yana nan kan hanyarsa ta zuwa ofishinsa.
Malam Mamman amininsa ne sosai, suna daraja juna. Suna shawartar juna a duk lokacin da za su gudanar da wani muhimmin al’amari. Haka suka taso tun suna yara, ajinsu daya tun daga firamare har zuwa sakandare. Inda suka rabu shi ne bayan sun kammala sakandare, inda Baba ya tafi Kwalejin Kimiyya da Fasaha ya yi difiloma kan harkar kasuwanci. Shi kuwa Mamman sai ya samu tafiya Jami’ar Bayero, inda ya yi digiri kai- tsaye. Ya nazarci dabarun koyar da darussan Hausa da Addinin Musulunci.
Ya karya kwana ke nan zai shiga makarantar, sai tayar motarsa daya, ta baya ta yi faci. Kan dole ya fito domin daukar matakin da ya dace. Ya sake buga wayar Mamman, ya sanar da shi halin da ya samu kansa. Kafin dan lokaci sai ga abokin nasa tafe bisa babur roba-roba.
“Karfen Nasara ba ka da tabbas. Mota mai gudu da mutum, kina kisa ana sake hawanki. Mota, jakar arziki!”
Kirarin da Mamman ya takarkare yana yi ke nan, lokacin da suka gama gaisawa da abokinsa.
“Kai dai bari,” inji Baba. “Muddin ka fito da mota, to tilas sai wani ya karu da kai, ko dai fetur, ko faci ko…”
“Mance da wani lissafi, bari in dauko mai faci, ya zo ya kwance tayar, kafin ya gama sai mu tattauna.” Ya katse abokinsa daga zancen da ya dauko.
Bayan ya dawo tare da mai faci, sai suka kebe a inuwar wata itaciyar dalbejiya. A lokacin da mai faci ke aikin kwance taya, su kuma sai suka dukufa tattaunawa.
***
A lokacin da mai faci ya takarkare yana aikin kwance taya, shi kuma Alhaji Baba da abokinsa Mamman Tela suna zaune a inuwar dalbejiya. Ba tare da bata lokaci ba suka shiga tattauna al’amura, wa ya mutu, wa ya dawo da sauran batutuwa da suka sha musu kai. Dama abin da suka saba da shi ke nan a kullum suka hadu.
“Yauwa, mu bar maganar ’yan siyasar nan da muka fara, mu koma kan batuna, wanda a yanzu yake neman kankane dukkan rayuwata.” Baba ya fadi haka ga abokinsa, a yayin da yake neman canja maudu’in da suke tattaunawa dangane da zaben ciyamomi da ke karatowa a Jihar Kano.
“Ina jin ka, dama ai na yi zaton da shi za mu fara, amma kai da kanka ka kawo batun zabe. Ni dai ban ma san dalilin da ka fara maida hankali kan siyasa ba, ko dai kana son tsundumawa ce?” Mamman ya tsokane shi.
“Wa, ni?” Baba ya yi wani zillo kamar wanda aka tsikara wa tsitaka a kwibi. “Allah tsari gatari da noma. Ai ni da shiga siyasa… to ba zan ce har abada ba, domin kana taka ne Allah kuma Yana tasa. Abin da ya sanya ka ga ina sako sha’aninsu, akwai wadanda muke hulda da su ta kasuwanci. Kwanaki ba na gaya maka cewa Alhaji Garba ya sayi dilolin atamfofi daga wurina ba? Ka san suna sayen kayayyaki suna rarraba wa magoya bayansu. Mu kuma ta nan muke amfana da su.”
“Ah to, yanzu na ji batu. To me kuma yake faruwa ne, kamar yadda kake kumu da shi haka?” Mamman ya fadi haka, a lokacin da yake tsefe guntun gemunsa da yatsun hannunsa na dama.
“Ta ina ma zan fara? Abin ne da yawa wai mai tsegumi ya shiga kasuwa. Ko ka san na samu kaina tsamo-tsamo cikin kogin soyayya?”
“Soyayya kamar yaya?” Mamman ya tambaya cikin mamaki.
“Kai dai bari. Abin ne za ka ji shi kamar almara amma ni dai a duk rayuwata, ban taba tsintar kaina cikin al’amarin son wata ’ya mace kamar wannan ba. Hatta shaukin soyayyar da ya kama ni lokacin da na hadu da uwargidata Farida, ban ji shi ba kamar yadda na hadu da wannan yarinyar, Saratu. Duka-duka shekaranjiya na fara haduwa da ita, amma ka san Allah, ji nake kamar mun shekara da fara soyayya.”
Mamman ya kyalkyace da dariya har da tuntsirawa. Dalili ke nan Baba ya dakata da magana, ya yi kasake yana kallon abokinsa yana tuntsira masa dariya.
“Don Allah kada ka maida ni zautacce mana. Yaya za ka yi ta kyalkyata mini dariya?”
“To, idan ba dariya zan yi ba, me kake zaton zan yi. Ai yadda na san yanayinka, na san irin matsayinka na dakusasshen ra’ayi game da soyayya. Dole ne in yi mamakin yadda ka fada kogin soyayar wata yarinya haka. Amma dai bari in saurara maka, inji yadda ta kaya.”